Tsohon Minista Ya Musanta Zargin Tinubu da Kisan ’Yar Takarar Gwamna a Lagos

Tsohon Minista Ya Musanta Zargin Tinubu da Kisan ’Yar Takarar Gwamna a Lagos

  • Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya musanta zargin cewa ya taba alakanta Shugaba Bola Tinubu da kisan kai
  • Ya ce Omoyele Sowore ne ya yi amfani da wata tsohuwar magana tasa domin kare kansa a karar batanci da ake yi masa
  • Fani-Kayode ya bukaci Sowore ya janye kalamansa ko ya fuskanci shari’a, yana mai yabawa salon jagorancin Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya musanta zargin batawa Bola Tinubu suna a shekarun baya.

Ana zargin wai Fani-Kayode ya taba danganta Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da hannu a kisan tsohon mai neman kujerar gwamnan jihar Lagos, Funso Williams.

Fani-Kayode ya musanta zargin Tinubu da kisan kai
Tsohon Minista, Femi Fani-Kayode da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Femi Fani-Kayode.
Source: Facebook

Fani-Kayode ya musanta bata sunan Tinubu

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Fani-Kayode ya ce Omoyele Sowore, ya ambaci wasu kalamai da ake zargin ya yi sama da shekaru 10 da suka wuce domin kare kansa a karar batanci da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Fani-Kayode ya bayyana cewa Sowore ya yi ikirarin cewa ya taba cewa Tinubu ne ke da alhakin kisan Williams, wanda aka kashe a gidansa da ke Ikoyi a watan Yulin 2006.

Ya ce:

“Shi (Sowore) ya yi ikirarin cewa na ce Shugaba Tinubu ya kashe Cif Funso Williams. Wannan ba gaskiya ba ne. Ban taba cewa Tinubu ya kashe Funso Williams ba.”

Ya kara da cewa kalaman da Sowore ya ambata sun fito ne daga lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2015, lokacin da yake dan jam’iyyar PDP.

Fani-Kayode ya ce daga baya ya janye kalaman, yana mai amincewa cewa ba su dace ba kuma za su iya janyo fassara ta daban.

A cewarsa:

“Ni ba Funso Williams ba ne; ba za a iya kashe ni kamar kaza ba.
“Na fadi wadannan kalamai shekaru 11 da suka wuce kuma tun tuni na janye su, na kuma amince cewa ba su dace ba kuma ana iya fassara su ta hanyar da ba ta dace ba.”
Fani-Kayode ya caccaki Sowore kan yi masa sharri
Tsohon minista a Najeriya, Femi Fani-Kayode. Hoto: Femi Fani-Kayode.
Source: Twitter

Fani-Kayode ya caccaki Sowore

Tsohon ministan ya bayyana kokarin Sowore na sake tayar da batun a matsayin alamar rashin mafita, yana mai cewa ba daidai ba ne a dogara da kalaman.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kunyata matarsa a bainar jama'a bayan ta yi kokarin kin sumbatarsa

Fani-Kayode ya kara da cewa ya bar jam’iyyar PDP shekaru shida da suka wuce, sannan ya shiga jam’iyyar APC a shekarar 2021, inda daga baya ya zama daya daga cikin manyan magoya bayan Tinubu.

Ya kuma nesanta tsohon hadimin Jonathan, Reno Omokri, daga batun, yana mai cewa Omokri ya janye suka da ya taba yi wa Tinubu bayan zaben 2023, sannan ya fara goyon bayan manufofin shugaban kasar.

Ya ce:

“Kokarin Sowore na hada ni ko Reno cikin wannan batu domin kare kansa abin dariya ne.”

Fani-Kayode ya bukaci Sowore da ya janye kalamansa game da Tinubu ko kuma ya shirya fuskantar shari’a, yana mai gargadin cewa sake tayar da batutuwan siyasa na baya ba zai taimaka masa a kotu ba.

'Na yi kuskure' - Fani-Kayode kan sukar Tinubu

Mun ba ku labarin cewa tsohon minista a Najeriya, Femi Fani-Kayode ya kare kansa kan rubutun da ya yi na suka Bola Tinubu a baya.

Fani-Kayode ya ce yana tare da jam'iyyar 'aladu' yana nufin jam'iyyar PDP kenan a lokacin da ya yi rubutun.

Amma ya ce a halin yanzu ya riga ya ga haske don haka tunaninsa ya canja kuma abin da ke gabansa shine aiki don nasarar Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.