Shugaba Tinubu Ya Kausasa Harshe kan Harin 'Yan Ta'adda a Kwara, Ya Dauki Mataki

Shugaba Tinubu Ya Kausasa Harshe kan Harin 'Yan Ta'adda a Kwara, Ya Dauki Mataki

  • Ana ci gaba da jimami da alhinin harin ta'addancin da 'yan ta'adda suka kai a jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana Gwamnan jihar Kwara, domin samun bayanai kan mummunan lamarin
  • Mai girma Tinubu ya yi Allah wadai da harin, tare da shan alwashin zakulo wadanda suka kai shi don su fuskanci hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kai a jihar Kwara.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kawar da duk masu ƙoƙarin raba ’yan Najeriya ta hanyar ta’addanci.

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin Kwara
Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin ranar tunawa da sojojin Najeriya Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kasar ya sanya a shafinsa na X a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairun 2027.

Kara karanta wannan

Turkiyya ta shirya taimakon Najeriya bayan kisan Musulmi kusan 200 a Kwara

Akalla mutane 100 ne aka kashe a kauyen Woro da ƙauyukan da ke makwabtaka da shi a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara a ranar Talata.

Me Bola Tinubu yace kan harin Kwara?

A cikin sanarwar, shugaban kasar ya ce ya gana da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, inda aka yi masa cikakken bayani kan lamarin.

Yayin da yake yin Allah-wadai da harin da ya bayyana a matsayin hari na matsorata kuma na dabbanci, Tinubu ya ce ’yan bindigar sun nuna rashin tausayi matuƙa wajen kai wa al’ummomi marasa kariya hari, a wani yunƙuri na ta’addanci da ya ce ba shi da makoma.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan ayyuka suna cin zarafin mutuncin ɗan Adam, addini da kimomin haɗin kan ƙasa na Najeriya.

“Jiya na bayar da umarnin tura bataliyar rundunar sojoji zuwa karamar hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, bayan mummunan harin da aka kai wa bayin Allah a Woro."
"Wannan sabuwar rundunar sojoji za ta jagoranci aikin ‘Operation Savannah Shield’ domin murƙushe waɗannan ’yan ta’adda tare da kare al’ummomin da ba su da kariya."

Kara karanta wannan

Bayan mummunan hari a Kwara, Tinubu ya sanya labule da Gwamnan jihat a Abuja

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya kadu kan manufar 'yan ta'adda

Ya ce abin da ya fi ba shi mamaki shi ne rahoton da ke nuna cewa an kai wa mutanen hari ne saboda sun ƙi amincewa da tilasta musu bin wata akida ta daban.

“Abin a yaba ne yadda mutanen yankin, duk da cewa Musulmai ne, suka yarda a tilasta musu wata akida wadda ke ingiza tashin hankali maimakon zaman lafiya da tattaunawa."

- Shugaba Bola Tinubu

Wane umarni Tinubu ya ba da?

Tinubu ya kuma bayar da umarnin haɗin gwiwa ta kut-da-kut tsakanin hukumomin tarayya da na jiha domin bai wa al’ummomin da abin ya shafa agajin gaggawa da tallafi, tare da tabbatar da cewa an farauto duk waɗanda ke da hannu a harin don gurfanar da su gaban shari’a.

“Na kuma bayar da umarnin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jiha domin samar da tallafi da agaji cikin gaggawa ga al’ummomin da abin ya shafa, tare da bin diddigin masu aikata wannan mummunan laifi a hukunta su. Ba za su tsira ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya girgiza kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya ba gwamnati mafita

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya gana da gwamnan jihar Kwara
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Shugaban Najeriya ya aika da ta'aziyya

Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan rayukan waɗanda suka rasu, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da al’ummar jihar Kwara da kuma gwamnatinta.

“Gwamnatin tarayya na tare da ku. Za mu kare al’ummominmu, mu kare kimominmu, kuma mu yi nasara kan duk masu ƙoƙarin raba mu ta hanyar ta’addanci."

- Shugaba Bola Tinubu

Sojoji sun sha alwashi kan harin Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi maganganu kan harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar Kwara.

DHQ ta bayyana cewa ta girgiza sakamakon rasa rayukan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba a hare-haren na 'yan ta'adda.

Daraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Samaila Uba ya jaddada cewa rundunar sojoji ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bin diddigin ’yan ta’addan da suka aikata wannan mummunan laifi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng