2027: Buba Galadima Ya Tona Shirin Sanatoci kan Dokar Zabe

2027: Buba Galadima Ya Tona Shirin Sanatoci kan Dokar Zabe

  • Jagora a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya shiga sahun masu sukar gyare-gyaren da majalisar dattawa ta amince da su a dokar zabe
  • Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa gyare-gyaren da aka yi wa dokar zaben za su iya kawo nakasu ga dimokuradiyyar Najeriya
  • Na hannun daman na Rabiu Kwankwaso ya nuna akwai manufa ta kashin kai da sanatoci ke son cimmawa ta hanyar amincewa da dokar zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ogun - Wani jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Buba Galadima, ya soki muhimman tanade-tanade na dokar zaɓe ta 2026 da majalisar dattawa ta amince da su.

Buba Galadima ya yi gargaɗin cewa gyare-gyaren da aka yi na iya raunana dimokuraɗiyyar Najeriya, su lalata sahihancin zaɓe, tare da buɗe ƙofa ga maguɗi gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya girgiza kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya ba gwamnati mafita

Buba Galadima ya soki majalisa kan dokar zabe
Buba Galadima na jawabi tare da jiga-jigan jam'iyyar NNPP Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Frontline, wani shirin al’amuran yau da kullum na tashar Eagle 102.5 FM, Ilese-Ijebu.

Buba Galadima ya soki Majalisar tarayya

Buba Galadima ya soki rage wa’adin doka da aka tanadarwa hukumar zaɓe INEC domin shirye-shiryen zaɓe, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda ba zai yiwu a aiwatar ba kuma mai haifar da koma baya.

"Ko da an yi lissafi, INEC ba za ta iya cika wa’adin kwanaki 360 ba, balle kuma a rage shi. Kuna ƙirƙirar matsin lamba mara amfani da zai iya kaiwa ga rikice-rikice.”

- Buba Galadima

Ya kuma yi Allah-wadai da majalisar tarayya bisa barin ikon yanke hukunci kan tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo a hannun INEC, yana mai cewa hakan na barin gibi da za a iya yin maguɗi.

“Ba su goge wannan tanadi ba. Sun bar shi ne kawai a hannun INEC, wanda ke ƙirƙirar damar yin maguɗi. Kokarin yin wayau kawai majalisar dattawa ta yi."

Kara karanta wannan

'APC ta tsorata, ta fara shirin magudi a zaben 2027,' ADC

- Buba Galadima

Buba Galadima ya zargi 'Yan majalisa

A cewarsa, da gangan ’yan majalisa suka sauya nauyin daukar alhaki zuwa INEC, duk da cewa hukumar ba ta da cikakken ’yanci.

“Suna so su tura alhaki ga INEC, amma INEC bangaren zartarwa ne ke naɗa ta, kuma ka san tabbas abin da gwamnati ke so shi ne INEC za ta fi yi."

- Buba Galadima

Buba ya fadi manufar 'Yan majalisar Najeriya

Buba Galadima ya zargi ’yan majalisa da kirkirar sabuwar dokar zaɓe domin kare muradunsu, maimakon amfanin ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa ba ta kawo wani sabon abu ba idan aka kwatanta da dokokin da suka gabata.

Buba Galadima ya yi tsokaci kan dokar zabe
Babban kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima Hoto: Buba Galadima
Source: Facebook
"Mun yi zaton duk lokacin da ake yin dokar zaɓe, za ta fi wadda ta gabata inganci. Amma wannan a bayyane yake cewa an yi ta ne domin kare muradun majalisar dattawa."
"Babu wani sabon abu a cikinta. Da sun bar Dokar Zaɓe ta 2022 yadda take, maimakon lalata ta saboda abin da suke shirin aikatawa a 2027.”

Kara karanta wannan

An samu sabani tsakanin Majalisar Dattawa da ta wakilai wajen gyara dokar zaben Najeriya

- Buba Galadima

Matsayar majalisa kan tura sakamako ta yanar gizo

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta ki amincewa da tsarin tura sakamakon zabe ta yanar gizo a nan take.

Majalisar dattawan ta yi watsi da gyaran da aka gabatar kan sashe na 60(3) na Kudirin gyaran dokar zaɓe wanda yake bukatar kwaskwarima.

Hakazalika majalisar ta kuma ki amincewa da kudirin hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ga masu saye da sayar da katin zaɓe na dindindin (PVC).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng