'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku, Sojoji Sun Sha Alwashi kan Harin Kwara

'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku, Sojoji Sun Sha Alwashi kan Harin Kwara

  • 'Yan ta'adda dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Kwara, wanda kusan kauyukan ba su taba ganin irinsu ba
  • Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ), ta sha alwashi kan harin na 'yan ta'adda wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane 100
  • DHQ ta bayyana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa mugayen d. Suka aikata danyen aikin sun fuskanci hukunci

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ), ta yi magana kan harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar Kwara.

Hedkwatar tsaron ta bayyana cewa 'yan ta'adda a Kwara da sauran wurare a kasar nan, ba za su ci bulus ba bayan kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Kara karanta wannan

Masu ibada da aka sace a Kaduna, sun fadi yadda rayuwa ta kasance a hannun 'yan bindiga

Sojoji sun sha alwashi kan harin 'yan ta'adda a Kwara
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Akalla mutane 100 aka kashe cikin rashin tausayi a Woro da ƙauyukan da ke makwabtaka da shi a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairun 2026.

Me Hedkwatar tsaro ta ce kan harin Kwara?

Manjo Janar Samaila Uba ya bayyana cewa rundunar sojoji ta matuƙar girgiza sakamakon rashin rayukan fararen hula da ba su yi laifin komai ba a abin da ya kira “sababbin hare-haren ta’addanci na tsoro da rashin imani.”

Ya jaddada cewa rundunar soji ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bin diddigin ’yan ta’addan da suka aikata wannan mummunan laifi.

"Rundunar soji tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen gano tare da hukunta waɗanda ke da hannu a wannan mummunan hari, haka nan da dukkan ’yan ta’adda a faɗin ƙasar nan.”

Kara karanta wannan

Ana fama da rashin tsaro, 'yan sanda sama da 5,000 za su ajiye aiki, an ji dalili

- Manjo Janar Samaila Uba

Sojoji sun ba 'yan Najeriya shawara

Babban jami’in sojan ya kuma bukaci ’yan kasa da su tsaya tsayin daka kan amannarsu ga kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma akidunsu na kashin kai.

Rundunar sojojin ta kuma yi kira ga dukkan ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko yanki ba, da su ƙi amincewa da kowace irin koyarwar akida da ƙungiyoyin ’yan ta’adda ke kokarin cusawa jama’a.

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Kwara
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
"Rundunar sojin Najeriya (AFN) na yaba wa jarumtar da al’ummomin Najeriya da dama suka nuna duk da kasancewa cikin fuskantar hari daga ’yan ta’adda."
“Wannan kyakkyawar juriyar ta sake bayyana a hannun mutanen Woro da ƙauyukan da ke makwabtaka da su, inda suka tsaya daram wajen yin biris da tashin hankali, tare da kin barin al’adunsu da biyayyarsu ga kundin tsarin mulki duk da barazanar da ake musu.”

- Manjo Janar Samaila Uba

Tinubu ya gana da Gwamnan Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya labule da Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya girgiza kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya ba gwamnati mafita

Ganawar ta su ta zo ne bayan da 'yan ta'adda suka kashe mutane sama da 100 yayin wasu hare-hare a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.

Harin 'yan ta'addan ya kasance ramuwar gayya ne bayan da al’ummar yankin suka ƙi halartar wa’azin tsagerun da kin rungumar akidarsu mai tsauri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng