Bayan Mummunan Hari a Kwara, Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamnan Jihar a Abuja

Bayan Mummunan Hari a Kwara, Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamnan Jihar a Abuja

  • Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya isa birnin Abuja bayan kai hari a jiharsa domin ganawa da shugaban kasa
  • Rahotanni sun ce ‘yan Boko Haram sun kashe fiye da mutum 100, sun kona gidaje da fadar basarake, yayin da Sarkin Woro ya bace
  • Shugaba Tinubu ya umurci tura rundunar sojoji Kaiama, ya kuma amince da sabon sansanin soja don kare al’umma daga ta’addanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya isa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja domin ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Gwamna ya tafi ganawa da Tinubu bayan hari a Kwara
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government.
Source: Twitter

Gwamnan Kwara ya shiga ganawa da Tinubu

Wannan ganawa ta zo ne bayan ‘yan ta’adda da ake zargin masu tsattsauran ra'ayi sun kashe fiye da mutum 100 a yankunan Kaiama na jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala

A daren Talata 4 ga watan Fabrairun 2026, ‘yan ta'adda da ake zargin mambobin Boko Haram ne suka kai hari kauyukan Worro da Nuku, suka kashe mazauna, suka kona gidaje da shaguna.

Har ila yau, an kona fadar basarake, yayin da Sarkin Worro, Saliu Umar, ya bace ba tare da an san inda yake ba.

Matansa biyu, wasu daga cikin ‘ya’yansa, limamin gari, shugaban makaranta da dalibai na daga cikin mutanen da aka kashe.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ramuwar gayya ne bayan da al’ummar yankin suka ƙi halartar wa’azin tsagerun da kin rungumar akidarsu mai tsauri.

An ce Sarkin Woro ya riga ya sanar da jami’an tsaro na soji game da ‘yan ta’adda a yankin kafin aukuwar harin.

Gwamna Abdulrazak ya gana da Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara. Hoto: Bayo Onaniga.
Source: Facebook

Umarnin da Tinubu ya ba jami'an tsaro

A ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar sojoji zuwa Kaiama domin ƙarfafa tsaro a yankin.

Shugaban kasar ya kuma amince da kafa sabuwar rundunar soja da za ta jagoranci 'Operation Savannah Shield' don yaki da ta’addanci.

Tinubu ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kiran sa da aikin rashin imani da cin zarafin bil’adama.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya girgiza kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya ba gwamnati mafita

Ya bayyana bacin ransa kan yadda aka kai hari kan mutanen da suka zaɓi zaman lafiya da Musulunci na gaskiya.

Mai girma Shugaban kasar ya bukaci haɗin kai tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin tallafawa al’ummomin da abin ya shafa.

Ya kuma bukaci a tabbatar an kamo wadanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci, kamar yadda Voice of Nigeria ta ruwaito.

Kwankwaso ya yi Allah-wadai da harin Kwara

A wani labarin, mutane da dama na ci gaba da jimamin kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi wa wasu mutane a kauyukan jihar Kwara.

Hare-haren ta'addancin sun jawo asarar rayuka sama da 100 na mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bi sahun yin Allah wadai kan mummunan harin, tare da ba shawararsa ga gwamnatin tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.