Tirkashi: An Yanke wa Tsohon Manajan Banki Hukuncin Daurin Shekaru 490 a Kurkuku
- Wata babbar kotun tarayya ta yanke wa Roberts Orya hukuncin daurin shekaru 490 a gidan yari saboda satar kudi da suka kai kimanin N2.4bn
- Tsohon shugaban bankin Nexim din ya fuskanci tuhume-tuhume 49 wadanda suka hada da cin amana da kuma karkatar da dukiyar jama'a
- Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa wannan hukunci zai zama darasi ga dukkan jami’an gwamnati dake amfani da mukamansu wajen yin sata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke wa Roberts Orya, tsohon babban manajan bankin Nexim, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 490.
A hukuncin da aka yanke a yau Alhamis, 5 ga Fabrairu, 2026, Mai Shari’a F.E. Messiri ya same shi da laifi kan tuhume-tuhume 49 da suka shafi cin amana.

Kara karanta wannan
INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP, ta yi zama da shugabannin jam'iyyu a Abuja

Source: UGC
Alkali ya yanke wa Orya hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10i akan kowane laifi guda ɗaya cikin 49 da ake tuhumarsa da su, cewar rahoton Leadership.
Tsohon manajan banki ya aikata zamba
Idan aka tattara waɗannan shekarun duka, sun kama jimillar shekaru 490 da zai shafe a gidan Jarun sakamakon zambar Naira biliyan 2.4.
Roberts Orya ya jagoranci bankin NEXIM ne tsakanin shekarar 2011 zuwa 2016, lokacin da ake zargin ya tafka wannan babbar damfara.
Binciken hukumar EFCC ya nuna cewa Orya ya yi amfani da muƙaminsa wajen karkatar da kuɗaɗe da kuma bayar da bashi ga kamfanonin bogi.
Waɗannan kamfanoni sun ƙi biyan bashin, wanda hakan ya janyo wa bankin NEXIM babban koma-baya da asarar kuɗi mai ɗumbin yawa.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa lauyanta, Samuel Ugwuegbulam, ya gabatar da hujjoji kwarara waɗanda suka tabbatar da laifin tsohon shugaban.
Shari'ar tsohon manajan banki
An fara gurfanar da Roberts Orya ne a gaban kotu tun a ranar 25 ga watan Nuwamba, shekarar 2021, bayan kammala bincike.
Tuhume-tuhumen da aka karanta masa sun haɗa da sojan gona, cin hanci, zamba, da kuma yin amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba, in ji rahoton The Nation.
Duk da cewa ya sha musanta dukkan zargin da ake masa, kotun ta gamsu cewa ya saci sama da Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari uku daga bankin.
Mai Shari’a Messiri ya bayyana cewa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 490 da aka yanke wa tsohon manajan zai zama gargaɗi ga duk wanda aka ba amana amma ya nemi ya ci ta.

Source: Twitter
Tasirin hukuncin ga Najeriya
Bankin Nexim shi ne babban bankin da ke tallafa wa masu fitar da kayan Najeriya zuwa ƙasashen waje don bunkasa tattalin arziƙi.
Gwamnati ta bayyana cewa irin wannan sata tana kawo cikas ga shirye-shiryen samar da ayyukan yi da kuma yin ruguza tattalin arziki.
A halin yanzu, an riga an tafi da tsohon shugaban bankin zuwa kurkuku domin fara gudanar da dogon zaman sa kamar yadda kotu ta umarta.
Wannan hukunci ya zo ne a matsayin wata babbar nasara ga hukumar EFCC wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a manyan ma'aikatu.
An yanke wa dalibi hukuncin kisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu a jihar Rivers, ta samu Damian Okoligwe, ɗalibin jami'ar Fatakwal (UNIPORT) da laifin kashe budurwarsa, Justina Otuene.
Okoligwe ya kasance dan aji hudu a sashen Petrochemical Engineering yayin da masoyiyarsa da ya kashe, Justina Otuene, ta ke aji uku a sashen Biochemistry na jami’ar.
Alkalin kotun, Justice Chinwe Nsirim-Nwosu, ya yanke wa Okoligwe hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an gabatar wa kotu isassun hujjoji da suka tabbatar da laifin.
Asali: Legit.ng

