Malami da Fararen Hula 4 da aka Kama da Zargin Hannu a Yunkurin Juyin Mulki a Najeriya

Malami da Fararen Hula 4 da aka Kama da Zargin Hannu a Yunkurin Juyin Mulki a Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutane da dama da ake zargi da hannu a zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu, ciki har da fararen hula hudu.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2025.

Biyo bayan tabbatar da lamarin, wasu rahotanni da suka fito sun sun nuna cewa an kama manyan sojoji, wasu jami'an tsaro da fararen hula.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hafsoshin tsaro
Hafsoshin tsaro yayin ganawa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin fararen hula da aka bayyana cewa an kama su zargin alaka da yunkurin juyin mulki.

1. An kama Sheikh Khalifa Zariya

Bayan kama shi, matar Sheikh Sani Khalifa Zariya ta ce ya bar gida da asuba, yana gaya mata cewa zai je Abuja domin wata bukata kuma zai dawo a ranar.

Kara karanta wannan

Da gaske sojojin Amurka sun cafke Sheikh Ahmed Gumi a filin jirgi? Gaskiya ta yi halinta

Matar ta bayyana cewa kama shi ya jefa ta cikin matsanancin tashin hankali, inda take ƙoƙarin daurewa kada hankalin yara ya tashi.

Wani dan malamin ya ce matsalar ta fara ne lokacin da mahaifinsa ya nemi cire kuɗi daga asusunsa na banki, inda aka sanar da su cewa EFCC ta rufe asusun.

Sheikh Sani Khalifa Zariya
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zariya. Hoto: Sheikh Sani Khalifa Zariya
Source: Facebook

A wani bidiyo da RFI Hausa ta wallafa a Facebook, dan malamin ya bayyana cewa bayan sun gama tattaunawa da EFCC a Abuja ne sojoji suka tafi da mahaifinsa.

Ana zargin wasu daga cikin wadanda suka shirya juyin mulkin sun ba shi kudi domin a yi masu addu'a, shehin ya karba ba tare da ya san abin da ake kitsawa ba.

2. An kama dan fim, Stanley Amandi

Ƙungiyar Fina-finai ta Najeriya (AGN) ta mayar da martani kan rahoton da ke cewa an kama mambanta, Stanley Amandi, bisa zargin rawar da ya taka a wani shiri na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon shugaban reshen AGN na jihar Enugu, Amandi, na daga cikin fararen hula da aka ruwaito an kama su dangane da zargin shirin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara bayan kashe Musulmai sama da 100

Da yake zantawa da the Cable, shugaban AGN, Emeka Rollas ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta san halin da Amandi ke ciki, kuma ya ce za su fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba.

Wani rahoton ya ce an bukaci Amandi ya yi amfani da furofaganda a fina-finasa wajen tallata juyin mulkin ta yadda idan an yi nasara zai samu karbuwa wajen mutane.

Dan fim Stanley Amandi
Jarumin fim da aka kama, Stanley Amandi. Hoto: Naija Gist
Source: Facebook

3. Juyin mulki: An cafke Ali Isah

Bayanai da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa daga cikin wadanda aka ce an kama akwai wani mai tukar motar asibiti mai suna Ali Isah.

Rahoton jaridar Business Day ya nuna cewa Ali Isah da aka kama mai tukar motar asibiti ne a fadar shugaban kasa, duk da cewa babu karin bayani game da shi.

Wani sashe na fadar shugaban kasa
Cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja. Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

4. An kama mai gyaran wutar lantarki

Cikin jerin mutane sama da 30 da hukumomin Najeriya suka kama bisa zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulki akwai wani mai gyaran wutar lantarki mai suna Umoru Zekeri.

Rahoto na musamman da jaridar Premium Times ta wallafa ya nuna cewa Umoru Zekeri na aiki ne da kamfanin Julius Berger a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPCL ya tona abubuwan da suka faru da matatun gwamnati

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu da aka so yi wa juyin mulki. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

An nemi a saki Sheikh Khalifa Zariya

A wani rahoto na dabam, kun ji cewa ana ci gaba da tattaunawa kan kama malamin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zariya, da aka yi a Najeriya.

Wata ƙungiya mai kare haƙƙin ɗan Adam ta nemi hukumomi da su hanzarta masa shari’a ko sakin sa ya koma wajen iyalansa.

Bisa wasu rahotanni, an yi zargin cewa an kama malamin ne bisa zargin karɓar kuɗi Naira miliyan 2 domin yin addu’ar samun nasara a shirin juyin mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng