Babbar Magana: Trump Ya Sake Gargaɗin Khamenei, Ya Faɗi Ɓarnar da Ya Yi wa Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei yayin da rikicin Amurka da Iran ke kara tsananta
- Trump ya ce Amurka na kara jibge kayan soji a kusa da Iran, yayin da tattaunawar diflomasiyya ke fuskantar barazana saboda rashin jituwa
- Shugaban ya yi ikirarin cewa hare-haren Amurka sun lalata cibiyoyin nukiliyar Iran, yana mai cewa hakan ya rage barazanar Iran a duniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya tura gargadi na musamman ga jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Donald Trump ya gargade shi da ya “ji tsoro” yayin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke kara tabarbarewa a halin yanzu.

Source: Getty Images
Gargadin da Trump ya yi wa Ayatullah Khamenei
Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da yan jaridu da CNN ta bibiya a ranar Laraba 4 ga watan Fabrairun 2026 da muke ciki.
Shugaba Trump ya ce ya kamata Khamenei ya tsorata sosai, saboda abin da zai fuskanta daga Amurka wanda yanzu alakarsu ta kara tsami.
Wannan gargadi ya zo ne yayin da Amurka ke kara tara sojoji da kayan yaki a kusa da Iran, tare da la’akari da daukar matakan soja domin raunata karfin da kasar ke da shi.
Duk da haka, Trump bai rufe kofar sulhu ba, sai dai tattaunawar da aka shirya yi tsakanin kasashen biyu na fuskantar rashin tabbas kan sharuddan zaman.
Shugaban ya ce barazanar da ya rika yi wa Iran ta taimaka wajen karfafa masu zanga-zangar cikin gida, ko da ba tare da shiga kai tsaye ba.
Ya ce:
“Mun tsaya musu. Kasar ta rikice yanzu saboda mu. Mun kai hari, mun lalata cibiyoyin nukiliyarsu gaba daya."

Source: Twitter
Yadda Amurka ta lalata cibiyoyin nukiliyar Iran
Trump ya kara da cewa da ba a lalata shirin nukiliyar Iran ba, da ba za a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba, cewar France 24.
Ya bayyana cewa kasashen Larabawa sun daina jin tsoron Iran bayan harin, yana mai cewa an kawo karshen barazanar da Iran ke yi musu.
Trump ya kuma yi ikirarin cewa Iran na kokarin sake farfado da shirin nukiliyarta a wasu wurare daban-daban a kasar da ta mallaka.
Ya ce Amurka ta gano shirin, inda ya gargadi Iran da cewa duk wani sabon yunƙuri zai jawo musu mummunan martani daga Amurka.
Amurka ta harbo jirgin leken asirin Iran
An ji cewa sojojin Amurka sun ce sun harbo wani jirgin leƙen asirin Iran bayan ya kusanci jirgin ruwan yaki na USS Abraham Lincoln wanda ya sake tarwatsa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake zargin cewa sojojin kasar Iran sun tsoratar da wani jirgin kasuwanci mai tutar Amurka a mashigar Hormuz.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka a dangantaka tsakanin Amurka da Iran kan batun tsaro da shirin mallakar makamin nukiliya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

