Sanusi II da Okonjo Iweala Sun Fito a Kundin Badakalar Epstein da aka Fitar

Sanusi II da Okonjo Iweala Sun Fito a Kundin Badakalar Epstein da aka Fitar

  • Wasu sakonnin imel sun nuna cewa an ambaci sunayen Ngozi Okonjo-Iweala da Sarki Muhammadu Sanusi II, a matsayin baƙi da za a gayyata liyafa tare da Jeffrey Epstein
  • Takardun da aka sake daga Amurka sun tayar da muhawara, musamman saboda yadda aka ga sunayen manyan mutane da kuma rashin sakin dukkan bayanan
  • Sai dai duk da haka, masu magana da yawun Okonjo-Iweala da Sarki Muhammadu Sanusi II a Kano sun bayyana cewa ba su san da wata gayyata ko hulɗa da Epstein ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wasu sabbin takardun imel da aka fitar daga tarin bayanan shari’ar marigayi, Jeffrey Epstein sun nuna cewa an taɓa ambaton sunayen wasu fitattun ‘yan Najeriya a wani shiri na liyafar sirri da aka tsara a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

An kashe 'yan Najeriya 4 bayan 'an yaudare su' taya Rasha yaki da Ukraine

Takardun da aka fitar na daga cikin kimanin takardu miliyan 3.5 da ke da alaƙa da Epstein, wanda ya shahara a Amurka a matsayin attajirin da aka taɓa yanke masa hukunci kan laifuffukan lalata kafin rasuwarsa a gidan yari a 2019.

Jeffrey Esptein Ngozi Okonjo-Iweala da Muhammadu Sanusi II
Ngozi Okonjo-Iweala a hagu, Jeffrey Esptein a tsakiya da Muhammadu Sanusi II a dama. Hoto: Getty Images|Sanusi II Dynasty
Source: Getty Images

Premium Times ta wallafa cewa bayyanar waɗannan takardu ya sake tayar da muhawara a duniya, musamman ganin yadda wasu muhimman bayanai.

Sakon imel da aka samu kan Epstein

Takardun sun nuna wata tattaunawa ta imel tsakanin Jeffrey Epstein da Jide Zeitlin, wani fitaccen ɗan kasuwa kuma mai zuba jari dan asalin Najeriya da ke Amurka.

A lokacin, Zeitlin shi ne shugaban kamfanin Tapestry, Inc., wanda ke da manyan kamfanonin kayan alatu kamar Coach, Kate Spade da Stuart Weitzman.

A cikin imel ɗin, Epstein ya nemi a ba shi jerin sunayen “mutane biyu ko uku masu basira” domin shirya wata liyafa “mai ban sha’awa” a watan Yuni na shekarar 2018.

A martaninsa, Zeitlin ya gabatar da jerin sunaye da suka haɗa da manyan mutane daga sassa daban-daban na duniya.

An ambaci Sanusi II, Okonjo-Iweala

Daga cikin sunayen da Zeitlin ya ambata akwai tsohuwar Ministar Kuɗi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala da kuma Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Abin da ya hana Epstein kasuwancin mai a Najeriya, ya shiya ganawa da Jonathan

A 2018, Okonjo-Iweala tana riƙe da manyan mukamai na ƙasa da ƙasa, ciki har da shugabancin hukumar Gavi, yayin da Sanusi ke kan karagar mulkin masarautar Kano.

Zeitlin ya bayyana Sanusi a matsayin “suna mafi ban sha’awa” a jerin, yana mai cewa shi ne “mafi basira” cikin mutanen da ya ambata.

Sauran sunayen da aka lissafa sun haɗa da tsohon babban mai ba Shugaban Amurka shawara, Steve Bannon, tsohon Firaministan Birtaniya, Tony Blair da dan uwan Sarkin Qatar, Mohammed bin Hamad bin Khalifa Al Thani.

Haka kuma akwai Tony Marx da Niall Ferguson, waɗanda Zeitlin ya bayyana a matsayin masu zurfin tunani da basira.

Martanin Sanusi II da Okonjo-Iweala

Duk da abubuwan da bayanan suka nuna, takardun ba su nuna cewa an aike da gayyata kai tsaye ko cewa an gudanar da liyafar ba.

Mai ba Okonjo-Iweala shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Nwabuikwu ya ce shugabar WTO ba ta taɓa sanin Epstein ba kuma ba ta da wata hulɗa da shi ko wani shiri na liyafa.

Haka nan kuma, Bashir Jentile da ke magana da yawun Sarkin Kano, ya bayyana cewa shi ma bai san da wata gayyata ko hulɗa tsakanin sarkin da Epstein ba.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya hallara taron sarakunan Afrika, ba a ga Aminu Ado ba

Sarki Muhammadu Sanusi II
Khalifa Muhammadu Sanusi II yayin wani taro a Legas. Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Sanusi II ya gargadi masu dukan mata

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi kakkausar suka game maza masu dukan matansu a Najeriya.

Sarkin ya bayyana cewa dokar kasa ba ta ba mutane damar dukan iyalansu ba ko da kuwa suna ganin al'adarsu ta ba su damar hakan.

Mai martaba Sanusi II ya bayyana cewa rashin wadatattun makarantu na daga cikin abubuwan da ke kara jawo yi wa mata auren wuri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng