Fadar Shugaban Kasa Ta Jero Wadanda Suka Jefa Mutane a Kangin Talauci a Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta zargi gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da laifi kan karuwar masu kuka da talauci a Najeriya
- Ana zargin dai akalla yan Najeriya miliyan 133 ke fama da talauci na rashin ababen more rayuwa kamar ilimi, kiwon lafiya da ruwan sha
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya goyi bayan kalaman tsohonKkaramin ministan kudi, Prince Clement Agba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Fadar Shugaban Kasa ta bayyana ce gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ne ke da alhakin jefa ’yan Nijeriya miliyan 133 cikin kangin talauci, ba gwamnatin tarayya ba.
Fadar shugaban Najeriyar ta ce gwamnoni da shugabannin kananan ya kamata a dorawa laifin karuwar adadin masu fama da talauci a Najeriya.

Source: Twitter
Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X wanda aka fi sani da Tuwita.
Masu laifi a jefa 'yan Najeriya cikin talauci
Cif Onanuga ya dora laifi kan jihohi da kananan hukumomi ne yayin da ya goyi bayan matsayar tsohon Karamin Ministan Kudi da Tsare-tsare, Prince Clement Agba.
Onanuga ya wallafa wani bidiyo na tattaunawar Agba, yana mai cewa:
“Wa ya kamata a dora wa alhakin ’yan Nijeriya miliyan 133 da ke cikin talauci? Gwamnatin tarayya? A’a. Jihohi? Eh. Kananan hukumomi 774? Eh.”
A cikin bidiyon, Agba ya yi bayanin cewa akwai bambanci tsakanin talaucin rashin kudi da kuma talaucin rashin ababen more rayuwa.
Tsohon Ministan ya yi ikirarin imanin ’yan Nijeriya miliyan 69.9 ne ke fama da talaucin rashin kudin da za su biya a kansu bukatu, wadanda ke rayuwa kasa da Dala biyu ($2) a rana.
Sai kuma talaucin rashin ababen more rayuwa, wanda Agba ya ce ya shafi mutane miliyan 133, kuma yana faruwa ne sakamakon rashin samun ilimi, ingantaccen kiwon lafiya, ruwan sha, da tsaftar muhalli.
Dalilan dora laifi kan jihohi da kananan hukumomi
Agba ya nanata cewa a karkashin tsarin mulkin Najeriya, samar da wadannan ababen more rayuwa aiki ne na gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi.
Ya soki gwamnatocin jihohi kan karkata dukkan ayyukan raya kasa zuwa manyan biranen jihohi tare da mancewa da yankunan karkara.
A cewarsa, rashin kula da asibitocin matakin farko (PHCs) da makarantun firamare ne ke kara ta'azzara talauci a matakin karkara.

Source: Twitter
Tsohon ministan ya jinjina wa gwamnati mai ci kan matakan gyara tattalin arziki da take dauka, ciki har da janye tallafin man fetur.
Ya amince cewa ko da yake manufofin suna da zafi, amma matakai ne da suka zama dole domin cigaban kasa, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Talakawa za su karu a Najeriya a 2026
A baya, mun kawo rahoton cewa an yi hasashen 'yan Najeriya miliyan 141 za su fada cikin talauci a wannan shekara ta 2026, wanda hakan ya kai kashi 62 na 'yan kasar.
Kamfanin PwC ne ya fitar da wannan rahoton, inda ya ce kashi 62 na al'ummar Najeriya, za su rasa arzikinsu, su fada talauci a shekarar nan ta 2026.
A cewar kamfanin PwC, hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin ƙaruwar kuɗaɗen shiga za su ci gaba da jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali kafin zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


