An Samu Sabani tsakanin Majalisar Dattawa da Ta Wakilai wajen Gyara Dokar Zaben Najeriya
- Alamu sun nuna an samu sabani a wasu sassan dokar zaben da aka yi wa garambawul a Majalisar dattawa da ta Wakilai
- Majalisun tarayyar sun kafa kwamitoci biyu da za su zauna su duba wadannan banbance-banbance domin a iya daidaita su
- Wannan dai na zuwa ne bayan Majalisun biyu sun amince da kudirin gyaran dokar zaben Najeriya yayin da ake shirye-shiryen 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa wanda ya ƙunshi mambobi daga jam’iyyu daban-daban domin daidaita ɓangarorin da aka samu saɓani a cikin ƙudirin gyaran dokar zaɓen Najeriya.
Kwamitin dai zai maida hankali kan sassan da aka yi sabani tsakanin Majalisar dattawa da Majalisar wakilai a dokar zaben da aka yi wa garambawul.

Source: Facebook
Mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya bayyana cewa wannan mataki ya fito ne daga wata wasiƙa da magatakardan majalisar, Dr. Yahaya Danzaria, ya aiko masa biyo bayan umarnin da ya samu daga shugabannin majalisa.
Mambobin kwamitin Majalisar Wakilai
Sanarwar ta nuna cewa Hon. Adebayo Balogun (shugaban kwamitin harkokin zaɓe na majalisar) ne zai jagoranci kwamitin.
Sauran mambobin sun haɗa da Hon. Fred Agbedi, Hon. Sada Soli, Hon. Ahmadu Jaha, Hon. Iduma Igariwey Enwo, Hon. Saidu Musa Abdullahi da Dr. Zainab Gimba.
Wannan kwamiti yana da alhakin zama da takwarorinsa na Majalisar Dattawa domin dinke ɓarakar da ke tsakanin dokokin da kowace majalisa ta amince da su, da nufin samar da tsayayyen kudiri ɗaya.
Majalisar Dattawa ta kafa nata kwamitin
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya riga ya bayyana sunayen mambobin kwamitin haɗin gwiwa na ɓangaren majalisar dattawa tun ranar Laraba.
Sanata Simon Bako Lalong ne zai jagoranci na Majalisar Dattawa, tare da sauran mambobi da suka kunshi, Sanata Niyi Adegbonmire, Sanata Mohammed Tahir Monguno da Sanata Adamu Aliero.

Source: Facebook
Sauran 'yan kwamitin sune Sanata Orji Uzor Kalu, Sanata Abba Moro, Sanata Asuquo Ekpenyong, Sanata Aminu Abbas da kuma Sanata Tokunbo Abiru.
Manufar wadannan kwamitoci da Majalisun biyu suka kafa shi ne tabbatar da cewa an samar da gyare-gyaren a dokar zabe da za su ƙara fito da gaskiya, kyakkyawar dabi’a, da kuma ƙarfafa amincewar al’umma ga tsarin dimuƙaraɗiyyar Najeriya.
Majalisa ta soke tura sakamako ta intanet?
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya musanta rahoton cewa Majalisar dattawa ta yi fatali da dokar tura sakamakon zabe ta na'ura kai tsaye.
Akpabio ya bayyana cewa majalisar dattawa ba ta yi watsi da tura sakamakon zabe ta na’ura ba a cikin gyaran da ta yi wa dokar zaben Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa fassarar da mutane suka yi kuskure ne, kuma tura sakamako ta yanar gizo har yanzu yana cikin dokar kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

