An Kashe Musulmai 75 saboda kin Karbar Bakuwar Akida a Kwara
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce akalla Musulmai 75 ne suka mutu a harin da ‘yan ta’adda suka kai a wasu kauyuka bayan al’ummar suka ki karbar bakuwar akida
- Harin ya afku ne a kauyukan Woro da Nuku, inda aka ce maharan sun tattara jama’a, suka daure musu hannu, sannan suka bude musu wuta, lamarin da ya girgiza Najeriya
- Gwamnan ya jaddada cewa abin da ya faru kitsan kiyashi ne tsantsa, yana mai bayyana hakan a matsayin abin Allah wadai da ke bukatar daukar mataki mai tsauri a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaiama, Kwara – Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar da cewa akalla mutum 75 ne aka kashe a wani mummunan hari da ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan Woro da Nuku da ke karamar hukumar Kaiama.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara yankin tare da shugabannin hukumomin tsaro da wasu mambobin majalisar zartarwa ta jihar, inda ya jajanta wa al’ummar da lamarin ya shafa.

Source: Facebook
A wani bidiyo da gwamnatin jihar Kwara ta wallafa a shafinta na X, an ga gwamnan a wata fada tare da jami’an soja da shugabannin al’umma, yana jajanta wa iyalan wadanda suka mutu.
Bayani kan mummunan harin jihar Kwara
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun afka kauyukan Woro da Nuku a yammacin Talata, inda suka rika tattara mazauna kauyukan, suna daure musu hannu kafin su bude musu wuta ba kakkautawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar harin, tana mai cewa an fara kai harin ne da misalin karfe 6:00 na yamma.
Ta ce tuni hukumomin tsaro suka tura jami’ai zuwa yankunan da abin ya shafa domin daidaita al’amura, sai dai ta ce har yanzu ana ci gaba da tantance adadin wadanda suka mutu da kuma binciken rahotannin bacewar wasu mutane.
An kashe Musulmai 75 saboda akida
Gwamna AbdulRazaq ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa mutum 75 ne aka kashe a harin, duk da wasu rahotanni sun ce sun fi 100.
Gwamnan ya ce al’ummar yankin sun kasance masu tsayin daka kan addininsu, kuma sun ki amincewa da wani gurbataccen tsari ko akida da ‘yan ta’adda ke kokarin tilasta musu.
Rahoton Arise News ya nuna cewa gwamnan jihar ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne saboda fushi da takaici, ganin cewa al’ummar sun ki sauya akidarsu.

Source: Original
Ya bayyana cewa wannan hari ya bambanta da abubuwan da aka saba gani na garkuwa da mutane ko kwace dukiya, yana mai cewa abin da ya faru kisan kiyashi ne tsantsa.
Ga bidiyon bayanin da ya yi a kasa:
Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da yadda wasu 'yan Boko Haram suka kashe mutane a Kwara.
Biyo bayan lamarin, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura bataliyar sojoji domin shiga dazukan jihar su kawar da 'yan ta'addan baki daya.
Shugaban kasar ya bukaci hadin kai tsakanin gwamnatin jihar da jami'an tarayya domin magance matsalolin tsaro da suka addabi al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

