Tinubu Ya Tura Bataliyar Sojoji Kwara bayan Kashe Musulmai Sama da 100

Tinubu Ya Tura Bataliyar Sojoji Kwara bayan Kashe Musulmai Sama da 100

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar sojoji zuwa Woro a karamar hukumar Kaiama, domin dakile hare-haren ‘yan Boko Haram
  • Harin da aka kai ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, inda rahotanni suka nuna sabani a alkaluman wadanda suka rasu, abin da ya kara tayar da hankali
  • Gwamnatin tarayya ta yi kira ga hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da na jihohi domin taimakon al’umma da hukunta masu aikata laifuffuka a fadin kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya umarci tura bataliyar sojojin Najeriya zuwa kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, biyo bayan mummunan harin da ‘yan Boko Haram.

Harin, wanda ya dauki awanni da dama, ya yi sanadin mutuwar mutane masu yawa, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin jimami da fargaba.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya saki tsohon dan bindiga Lankai, ya tara jama'a ya yi jawabi

Shugaban Najeriya da hafsoshin tsaro
Shugaba Bola Tinubu da hafsoshin tsaron Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bayanan umarnin shugaban kasa sun fito ne ta bakin kakakin fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, wanda ya bayyana aniyar gwamnati na dakile ta’addanci da kare fararen hula a shafinsa na X.

Bola Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara

A cewar Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya ce sabon rundunar sojojin da aka tura za ta jagoranci Operation Savannah Shield domin murkushe ‘yan ta’adda da kuma kare al’ummomin da ba su da kariya.

Shugaban kasar ya yi kakkausar suka kan harin, inda ya bayyana shi a matsayin abin kunya da rashin tausayi, yana mai kiran ‘yan ta’addan da marasa imani da tausayi.

Ya ce manufar tura sojojin ita ce tabbatar da tsaro mai dorewa a yankin da kuma hana sake aukuwar irin wannan mummunan hari.

Shugaba Tinubu ya ce Musulmai aka kashe

A cikin sanarwar, Onanuga ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa galibin mutanen da aka kashe Musulmi ne da suka ki amincewa da tilastawa shiga akidar da ke karfafa tashin hankali maimakon zaman lafiya da tattaunawa.

Kara karanta wannan

Binciken yunkurin juyin mulki ya sa an kama tsohon Janar mai rike da sarauta

Shugaban kasar ya yaba wa wadanda suka rasa rayukansu bisa tsayin daka da suka nuna wajen kin karbar tsattsauran ra’ayin addini da ‘yan ta’addan ke yadawa.

Taswirar jihar Kwara
Taswirar jihar Kwara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya kuma bukaci hadin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jiha domin tallafa wa al’ummar da abin ya shafa tare da tabbatar da cewa masu laifin ba za su tsira ba.

Mutanen da aka kashe a harin

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa harin ya fara ne da misalin karfe 5:00 na yamma a ranar Talata, inda ‘yan ta’addan suka rika kai farmaki tsawon sa’o’i kafin su janye da sassafe.

Premium Times ta ce wasu rahotanni sun ce ‘yan Boko Haram karkashin jagorancin Mallam Sadiku ne suka kai harin, inda wasu kafafen yada labarai suka ce kimanin mutane 170 ne suka mutu.

Sai dai gwamnatin jihar Kwara ta ce alkaluman wadanda suka rasu sun kai 75, yayin da Red Cross ta tabbatar da mutuwar 162 zuwa yammacin ranar Laraba.

Turji ya saki Audu Lankai a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa yaran babban 'dan bindiga, Bello Turji sun saki dan ta'adda da ya tuba, Audu Lankai a karamar hukumar Jibia ta Katsina.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

Rahotanni sun nuna cewa mutanen yankin sun shiga fargaba bayan kama Lankai da yaran Turji suka yi, sun fara rufe kasuwa da wuri da takaita zirga-zirga.

Bayan sakin Lankai, daruruwan jama'a sun taru, inda ya yi masu bayani game da rungumar zaman lafiya da afuwa a kan duk abin da ya wuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng