Ma'aikata Sun Fara Cin Moriyar Dokokin Haraji, An Fara Gani a Albashin Janairu
- Rahotanni sun nuna cewa sababbin dokokin haraji sun fara rage nauyin haraji ga yawancin ma’aikata a Najeriya
- Wannan ya sa wasu sun fara ganin karin albashi a kan wanda suka saba karba a watanni baya daga ma'aikatun da suke aiki
- 98% na ma’aikata za su biya ƙasa da harajin da aka saba cire masu ko ma a cire gaba daya harajin da suke biya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ma’aikata a Najeriya na fara cin gajiyar sababbin dokokin haraji da suka fara aiki a watan Janairu.
Wadansu daga cikin ma’aikatan bangaren gwamnati da masu zaman kansu sun karɓi albashi sama da wanda ake ba su a baya saboda rage harajin.

Source: Twitter
TABLE OF CONTENTS
Premium Times ta ruwaito cewa ana ganin sababbin dokokin haraji da aka sanya wa hannu a ranar 26 ga Yuni, 2025 a matsayin masu inganta rayuwar taklaka.

Kara karanta wannan
Tinubu ya sanar da matsaya kan janye cire tallafi da sauran manufofin tattalin arziki
An fara cimma manufar dokokin haraji
Daga cikin manyan manufofin dokokin harajin akwai kare masu ƙaramin albashi, bisa fahimtar cewa tsarin haraji na adalci bai kamata jibga wa mai karamin karfi nauyi ba.
Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin Shugaban kasa a kan gyara dokokin haraji, a watan Oktoban bara ya ce kusan 98% za su mori tsarin harajin.
Ya ce na ko dai za a cire su daga tsarin 'Pay As You Earn' (PAYE) gaba ɗaya, ko kuma za su biya haraji ƙasa da yadda suke biya a baya a ƙarƙashin sabuwar doka.
Sabuwar doka ta ware ma’aikatan da ke samun kuɗin shiga a shekara da bai wuce Naira miliyan 1.2 ba daga biyan haraji.

Source: Facebook
Haka kuma, ma’aikatan da ke karɓar mafi ƙarancin albashi za a cire su daga tsarin biyan harajin kai tsaye.
An tanadi tsarin haraji yadda duk abin da ya haura wannan adadi har zuwa sama da Naira miliyan 50 zai bada haraji har 25%.
Ma’aikatan da ke samun tsakanin Naira miliyan 1.2 zuwa Naira miliyan 20 a shekara za su biya haraji ƙasa da yadda suka saba a sabon tsarin.
Binciken jaridan ya nuna cewa wasu ma’aikata sun bayyana cewa an fara samun abin da ake so bayan sun fara ganin canji a albashinsu.
Ololade Ruel Jethro, ma’aikaci a kamfanin Zoomlion Nigeria Limited da ke Legas ya ce:
“Sabon tsarin haraji ya yi tasiri mai kyau ga albashina na watan Janairu. Albashina na wata ya ƙaru, wanda nake ganin hakan ya samo asali ne daga sababbin rangwamen haraji da cire-cire."
Manyan ma'aikata sun ga ragi a albashinsu
Sai dai Legit Hausa ta bibiya kafofin sada zumunta inda ta ci karo da wasu manyan ma'aikata suna kukan cewa albashin da ake biyansu ya ragu a watan Junairun 2026.
Wani bawan Allah a dandalin X ya fito yana tir da yadda ya ga an cire kusan N30, 000 a albashinsa da sunan haraji.
Haka zalika wani matashi a shafin Facebook ya bayyana cewa ya ga kari kadan a kudinsa, amma wani babban ma'aikaci ya ga akasin haka, albashinsa ya ragu ne a bana.
NLC na son a kara wa ma'aikata albashi
A wani labarin, mun wallafa cewa NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta duba albashin ma’aikata a fadin kasar nan saboda tsadar rayuwa da hauhawar farashi.
Kungiyar ta bayyana cewa duk da aiwatar da wasu tsare-tsaren tattalin arziki, yawancin ma’aikata na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayan abinci.
A sakon sabuwar shekara ta 2026 da ta aikewa ma’aikata da al’ummar Najeriya baki daya, NLC ta ce shekarar 2025 ta kasance mai matukar wahala ga talakawa da ma’aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

