'Mutane Sun Yi Ta Kansu,' Halin da Ake ciki a Garin da Aka Kashe Sojan Najeriya

'Mutane Sun Yi Ta Kansu,' Halin da Ake ciki a Garin da Aka Kashe Sojan Najeriya

  • 'Yan bindiga sun kashe soja da wasu fararen hula biyar a garin Zurak dake Jihar Filato yayin da wasu sojoji uku suka bace bayan harin
  • Daruruwan mazauna garuruwan Wase sun tsere daga gidajensu saboda fargabar karin wasu hare-haren 'yan bindiga a yankunansu
  • Gwamnati ta tura karin jami'an tsaro domin kwantar da tarzoma amma mazauna yankunan sun dage cewa ba za su koma gida yanzu ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Mazauna garuruwan Zurak da Sabon Gari dake gundumar Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta Jihar Filato, suna ci gaba da tserewa daga gidajensu sakamakon hare-haren da aka kai masu.

Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar soja ɗaya da fararen hula biyar, yayin da har yanzu ba a san inda wasu sojoji uku suke ba bayan fafatawa da maharan.

Kara karanta wannan

Ana murna sulhu ya fara aiki, 'yan bindiga sun shiga gari sun kashe akalla mutune 20

'Yan bindiga sun kashe soja da fararen hula a harin da suka kai Filato.
Wani ayarin sojojin Najeriya da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda yayin da suke bakin aiki. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Wani shugaban matasa a Wase, Shapi’i Sambo, ya tabbatar da cewa an kwashe gawar sojan da aka kashe zuwa birnin Jos, kamar yadda rahoton Arise News ya nuna.

Yadda maharan suka farmaki sojoji

Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigar sun fara kai hari ne kan shingen binciken sojoji dake garuruwan kafin su shiga cikin gari.

Bayan sun fatattaki sojojin, sai maharan suka banka wa gidaje da shaguna wuta, sannan suka kwashe kayan abinci da sauran abubuwa masu daraja na jama'a.

Jibrin Isa, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa:

“Sun kwashe kayayyaki a kusan dukkan shagunanmu, sannan suka nufi Zurak inda suka sake kai hari kan shingen binciken sojoji tare da kashe mutane.”

Daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu

A halin yanzu, garin Zurak ya zama kamar kufai domin dukkan mazauna garin sun tsere zuwa maƙwabta domin neman tsira da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

Duk da cewa an tura ƙarin jami'an tsaro daga garin Wase zuwa waɗannan ƙauyuka, mazauna yankin sun ce ba su amince da yanayin zaman lafiya a garuruwansu ba.

An ga maza da mata har ma da ƙananan yara suna tafiya a ƙasa ɗauke da kayayyakinsu, inda suka nufi ƙauyen Kampani dake kusa domin fake wa maharan.

Jaridar Daily Trust ta rahoto wani Ya’u Usman, mazaunin Zurak, ya bayyana cewa:

“Dole ne mu tsere daga gidajenmu domin rayuwarmu tana cikin garari. Ƴan bindigan suna zuwa da yawa kuma suna fin ƙarfin jami'an tsaro.”
Mazauna wasu garuruwan Filato sun tsere daga gidajensu bayan hare-haren 'yan bindiga.
Taswirar Filato, jihar da 'yan bindiga suka kashe sojan Najeriya da fararen hula. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yankin Wase na fuskantar matsalar tsaro

Hukumar tsaro ta "Operation Enduring Peace" ta bakin Kyaftin JA John, ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan wannan lamari da ya faru.

Wannan harin na zuwa ne watanni kaɗan bayan an sace matafiya 28 daga garin Zak a watan Disamba 2025, waɗanda har yanzu wasu ba su dawo gida ba.

Yankin Wase ya kasance cikin matsalar tsaro sakamakon dazukan dake maƙwabtaka da Jihar Taraba da kuma Bauchi waɗanda ƴan bindiga ke amfani da su.

Kara karanta wannan

A rana guda, 'yan bindiga sun kashe fiye da mutane 50 a wasu jihohin Arewa 2

Mutane sun yi gudun hijira a Gombe

A wani labari, mun ruwaito cewa, sama da mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu biyo bayan munanan hare-haren 'yan bindiga a masarautar Pindiga.

Hare-haren sun shafi Garin Galadima da wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Akko, jihar Gombe inda jama'a suka yi hijira domin tsira da rayukansu.

Iyalan da abin ya shafa daga Garin Galadima, Lumbo, da Shulto yanzu haka suna gudun hijira a garuruwan Tumu, Kashere, da Pindiga, inda ke da aminci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com