Shugaban NNPCL Ya Tona Abubuwan da Suka Faru da Matatun Gwamnati

Shugaban NNPCL Ya Tona Abubuwan da Suka Faru da Matatun Gwamnati

  • Shugaban kamfanin mai na kasa, Bayo Ojulari ha bayyana dalilan da suka jawo gwamnati ta rufe matatun mai
  • Gwamnatin Najeriya dai ta dakatar da ayyukan matatun mai da suke karkashinta saboda tarin asara da ake yi
  • Bayo Ojulari ya kara da cewa wannan ya sa NNPCL ya fara sauya salo zuwa kasuwanci don a samu riba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa gwamnati ta yi asara sosai a wajen tafiyar da matatun man da ke hannunta.

Bayo Ojulari ya ce wannan babbar asara da ake tafka wa ta sa gwamnati ta yanke shawarar dakatar da ayyukansu domin hana ci gaba da salwantar da dukiyar ƙasa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamnati ta bada umarnin rufe makarantu a fadin jihar Kogi

Shugaban NNPCL ya ce an yi asara sosai a gudanar da matatun man NNPPL
Bayo Ojulari, Shugaban kamfanin NNPCL Hoto: NNPC Limited
Source: Getty Images

Jariar Punch ta wallafa cewa Ojulari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairu, 2026 a Abuja yayin wani taro a kan makamishi.

NNPCL ta fuskanci matsala da matatunta - Ojulari

Vangard ta ruwaito cewa Bayo Ojulari ya yi bayani dalla-dalla kan hakikanin halin kasuwanci, ayyuka da harin da matatun man NNPCL suka shiga.

A cewarsa, babu laifi fushin da ‘yan Najeriya ke nunawa kan matatun man, la’akari da yawan kuɗin jama’a da aka zuba a cikinsu tsawon shekaru don a samu sauki.

Ojulari ya ce:

“Game da matatun man, ‘yan Najeriya sun yi fushi. An kashe kuɗi masu yawa, kuma an sa rai da samun ci gaba. Don haka muna jin matsin lamba a kan ayyukanmu."

Ya kara da cewa a lokacin da ya shiga ofis, harkar tace mai ba ita ce babban fagen ƙwarewarsa ba, kasancewar yawancin aikinsa ya kasance a ɓangaren bincike da haƙo mai.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, Gwamnatin Tinubu ta rufe bakin matasan N Power

Dalilan dakatar da ayyukan matatun NNPCL

Ojulari ya bayyana cewa a lokacin da tawagarsa ta fara aikin bincike, ta gano yadda matatun ke ci gaba a aiki, amma anajawo asarar kudi mai yawa.

Ya ce:

“Abu na farko da ya fito fili, kuma ina so in faɗi wannan a bayyane, shi ne muna aiki ne cikin babbar asara ga Najeriya. Muna ɓata kuɗi."

Ya ƙara da cewa NNPC na shigar da ɗanyen mai cikin matatun kowane wata, amma ana aiki da 50% zuwa 55%, wanda ke jawo masu asara.

Bayo Ojulari ya ce:

“Muna kashe kuɗi da yawa wajen ayyuka da ‘yan kwangila. Amma idan ka duba ribar, asara kawai ake yi."
Ojulari ya ce dole gwamnati ta rufe matatun
Shugaban kamfanin mai na NNPCL, Bayo Ojulari Hoto: NNPC Limited
Source: Twitter

Abin da ya fi tayar masa da hankali, a cewarsa, shi ne rashin wani tabbataccen shiri na dawo da kudin da aka dade ana zuba wa a cikin matatun.

Saboda haka, Ojulari ya ce matakin farko da gwamnatinsa ta ɗauka shi ne dakatar da ayyukan matatun domin hana ƙarin asara.

Kara karanta wannan

NNPCL ya bi sahun matatar Dangote, ya kara farashin litar man fetur

Ojulari ya ce dakatar da ayyukan matatun mataki ne mai sarkakiya ta fuskar siyasa, duba da yadda a tarihi ake matsa wa NNPCL domin samun wadatar man fetur.

An saka matatun man NNPCL a kasuwa

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a halin yanzu ta buɗe ƙofa ga masu zuba jari da ke sha’awar sayen matatun man fetur na Warri, Fatakwal da Kaduna.

Mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a taron makamashi na ADIPEC da aka gudanar a birnin Abu Dhabi.

Ta ce gwamnati na duba dukkannin hanyoyin da za su tabbatar da inganci da tsari a ɓangaren mai, ciki har da bai wa masu zaman kansu damar mallaka ko gudanar da matatun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng