Abin da Majalisar Dattawa ba Ta Yarda da Shi ba game da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

Abin da Majalisar Dattawa ba Ta Yarda da Shi ba game da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

  • Sanata Godswill Akpabio ya musanta rahoton cewa Majalisar dattawa ta yi fatali da dokar tura sakamakon zabe ta na'ura kai tsaye
  • Shugaban Majalisar dattawan ya ce mutane ba su fahimci matsayar da suka dauka kan wannan tanadi ba a gyaran dokar zaben Najeriya
  • Akpabio ya ce sun ki yarda su wajabta tura sakamako ta intanet kai tsaye, maimakon haka sun bar tanadin yadda yake a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi karin haske kan rahotannin da suke yawo cewa sanatoci sun yi fatali da dokar tura sakamakon zabe ta intanet.

Sanata Akpabio ya bayyana cewa majalisar dattawa ba ta yi watsi da tura sakamakon zabe ta na’ura ba a cikin gyaran da ta yi wa dokar zaben Najeriya.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Majalisa ta cimma matsaya kan tura sakamako ta yanar gizo

Shugaban Majalisa.
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabi yayin zaman sanatoci a Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Abin da majalisa ta ki amincewa da shi

Sai dai Shugaban Majalisa ya tabbatar da cewa sun ki amincewa ne da mayar da tura sakamakon zabe ta na'ura zuwa shafin tattara sakamako IREV ya zama dole, in ji rahoton Tribune Nigeria.

Akpabio ya yi wannan karin bayani ne jim kadan bayan majalisar ta amince da kudirin gyaran dokar zabe biyo bayan wani dogon zama da aka kwashe kusan sa'o'i hudu da rabi ana gudanarwa.

Sanatoci sun tafka muhawara kan dokar zabe

Rahotanni sun nuna cewa sanatoci sun shafe tsawon lokaci suna tafka muhawarar kan wannan sashe mai cike da rudani (Sashe na 60, Karamin Sashe na 3), inda aka ce sun fara ne daga karfe 2:00 na rana har zuwa 6:26 na yamma.

Vanguard ta ce hakan sanya aka fara rade-rade a kafafen sadarwa na zamani cewa mambobin majalisar dattawan sun kada kuri'ar nuna rashin amincewa da tura sakamako ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta rufe bakin masu surutu, ta yi gyara a dokar zaben Najeriya

Maimakon haka, majalisar ta tabbatar da tanadin da ke cikin tsohuwar dokar zabe, wanda ke bai wa hukumar INEC damar tantance hanyar da za a bi wajen tura sakamako da bayanan masu zabe.

Majalisa ta soke tura sakamako ta intanet?

Da yake mayar da martani, Sanata Akpabio ya jaddada cewa fassarar da mutane suka yi kuskure ne, kuma tura sakamako ta yanar gizo har yanzu yana cikin dokar kasa.

Ya bayyana cewa:

"Abokan aiki, kafafen sadarwa sun cika da rahotannin cewa Majalisar Dattawa ta yi watsi da tura sakamakon zabe ta yanar gizo, wannan ba gaskiya ba ne.
"Abin da muka yi shi ne mun tsaya a kan tanadin tura sakamakon ta yanar gizo wanda yake cikin doka tun 2022 kuma aka yi amfani da shi."
"Don haka, don Allah kada ku yarda mutane su rude ku. Wannan majalisa a karkashin jagoranci na ba ta cire tura sakamako ta yanar gizo ba, ni ma ina da sha'awar hakan tunda zan shiga zabe mai zuwa. Mun bar tanadin a yadda yake ne kawai.
Majalisar dattawa.
Zaman Majalisar dattawa karkashin jagorancin Sanata Godswill Alpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Majalisa ta yi gyare-gyare a dokar zabe

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin gyara kundin dokokin zaben Najeriya.

Kara karanta wannan

Nesa ta matso kusa: Hukumar INEC ta kammala tsara jadawalin babban zaɓen 2027

An yi gyare-gyare ga wasu daga cikin sassan dokar yayin da aka bar mafi akasarin sauran yadda suke a cikin shawarwarin da aka gabatar gaban Majalisar.

Daya daga cikin manyan gyare-gyaren da aka gudanar shi ne rage lokacin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar gudanar da zaɓe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262