Majalisar Dattawa Ta Rufe Bakin Masu Surutu, Ta Yi Gyara a Dokar Zaben Najeriya

Majalisar Dattawa Ta Rufe Bakin Masu Surutu, Ta Yi Gyara a Dokar Zaben Najeriya

  • Majalisar dattawan Najeriya ta kammala gyare-gyare a dokar zaben Najeriya yayin da aka fara surutu kan jinkirin da aka samu
  • Bayanai sun nuna cewa Majalisar dattawa ta yi fatali da bukatar maida tsarin tura sakamakon zaben ta intanet ya zama dole
  • Sai dai bayan sauraron Sanata Tahir Monguno, Majalisa ta amince da rage lokacin sanarwar shirin zabe daga kwanaki 360 zuwa 180

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin gyara kundin dokokin zaben Najeriya, wadda aka yi a shekarar 2022.

Majalisar dattawa ta kammala aiki kan gyare-gayren da aka yi wa dokar, tare da amincewa da sabuwar dokar zabe ta 2026.

Majalisar dattawa.
Zauren Majalisar dattawa a lokacin da sanatoci ke tsakiyar zama a Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar ta amince da ƙudirin ne bayan duba tare da sahalewa kan bangarori guda 155 da ke cikin dokar.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Majalisa ta cimma matsaya kan tura sakamako ta yanar gizo

An yi gyare-gyare ga wasu daga cikin sashen, yayin da aka bar mafi akasarin sauran yadda suke a cikin shawarwarin da aka gabatar gaban Majalisar.

Muhimmin gyaran zaben da Majalisa ta yi

Daya daga cikin manyan gyare-gyaren da aka gudanar shi ne rage lokacin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar gudanar da zaɓe.

Majalisar dattawa ta amince da rage wannan lokaci daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180.

Wannan ya biyo bayan amincewa da wani jawabi da Sanata Tahir Monguno ya gabatar, inda ya bukaci a rage kwanaki 360 da aka tanada a baya zuwa kwanaki 180.

Dalilin rage lokacin sanarwar zabe

Sanata Monguno ya yi bayanin cewa rage lokacin ya zama dole ne domin ba wa hukumar INEC damar cika sharuddan wallafa sanarwar zaɓen.

Ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da kwanaki 360 na tsohuwar dokar, lokaci ya riga ya ƙure na sanarwar babban zaɓe mai zuwa.

An gyara batun tura sakamako ta intanet?

A wani bangaren kuma, Majalisar Dattawa ta yi watsi da wani yunkurin gyara ga Sashe na 60, Karamin Sashe na 3, wanda ya nemi a mayar da tura sakamakon zabe ta intanet ya zama dole.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

A cewar tashar Channels tv, wannan gyaran zai bukaci jami’an INEC su tura sakamakon zabe kai-tsaye daga kowace rumfa zuwa shafin tattara sakamako watau IREV a daidai lokacin da aka kammala.

Wannan na nufin tura sakamakon zai kasance ne bayan jami’in zabe ya sanya hannu da hatimi a kan takardar sakamako ta Form EC8A, sannan wakilan jam’iyyu su ma su sanya hannu.

Majalisar dattawan Najeriya.
Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Maimakon amincewa da wannan gyaran, Majalisar Dattawan ta gwammace ta bi tsohon tsarin da ke cikin dokar zabe, wanda ya bayyana cewa:

“Jami’in gudanar da zabe zai tura sakamakon zabe, gami da jimillar adadin masu jefa kuri’a da aka tantance da kuma sakamakon kuri’un da aka kada, ta hanyar da INEC ta gindaya.”

Majalisa za ta gyara tsarin kasafta kudin shiga

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta fara yunkurin ƙara yawan kason da ake bai wa gwamnatin tarayya idan an tattara kudin shiga a kowane wata.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da majalisar ke yi cewa kuɗin da ake bai wa gwamnatin tarayya ya yi kadan.

Duk da kasancewar gwamnatin tarayya na da mafi girman kaso, majalisar dattawa ta ce akwai buƙatar ƙarin kuɗi saboda ƙaruwa da nauyin ayyuka da ke wuyanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262