Zargin Ta'addanci: Dalung Ya Kalubalanci Kama Malami da DSS Ta Yi
- Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya kalubalanci gwamnatin tarayya a kan shari'a da tsohon Ministan shari'a
- Dalung ya ce ya kamata a gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci tare da Malami ba wai a kai shi da dansa kawai kotu ba
- Korafinsa na zuwa a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ke shari'a da Abubakar Malami bisa zargin alaka da ta'addanci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya soki gwamnatin tarayya kan shari’ar da ake yi wa tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.
Ya tambayi gwamnatin dalilin da ya sa aka gurfanar da Malami shi kaɗai ba tare da waɗanda ake zargin sun ɗauki nauyin ta’addanci ba.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya fadi dalilan da suka sa ba zai yi shiru a kan harkokin gwamnati ba

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Dalung ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan shari’ar da ke gudana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Dalung ya soki gwamnati a kan Malami
Daily Post ta ruwaito cewa Dalung ya ce daga tuhumar da aka karanta a kotu, ya fahimci cewa ana tuhumar Malami ne saboda ya ƙi gurfanar da waɗanda ake zargin masu ɗaukar nauyin ta’addanci ne a lokacin da yake Antoni Janar.
A cewarsa, wannan ya haifar da manyan tambayoyi kan sahihancin matakin da gwamnati ta ɗauka na gurfanar da shi a gaban kotu da fara shari'a a kan alaka da yan ta'adda.
A cewar Dalung, idan har ana zargin Malami da ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, to ya kamata waɗannan mutanen su ma su kasance a gaban kotu.
Ya ce akwai jerin sunayen waɗanda aka miƙa wa gwamnatoci daban-daban a baya, amma ba a ga inda suke ba ballantana a fara batun shari'a.

Source: Getty Images
Dalung ya ambaci jerin sunayen da ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da kuma wasu jerin da aka ce an miƙa wa wannan gwamnati daga wata ƙasa makwabta.
Ya tambaya ina waɗannan masu ɗaukar nauyin ta’addanci suke, me ya sa ba a gurfanar da su ba. A ra’ayinsa, bai dace Malami ya tsaya shi kaɗai a gaban kotu ba a kan wannan lamari.
Dalung ya yi mamakin kai iyalin Malami kotu
Sololmon Dalung ya kuma yi mamakin ganin an gurfanar da ɗan Malami, Abdulaziz, tare da tsohon ministan tarayyar a gaban kotun.
Ya tambaya ko ɗan nasa ne ya hana mahaifinsa gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, har ya sa aka haɗa shi cikin shari’ar.
Wannan mataki, a cewarsa, yana buƙatar ƙarin bayani ga ’yan Najeriya domin a san dalilan da suka sa aka dauki matakin da aka dauka.
DSS ta gurfanar da Abubakar Malami da ɗansa a gaban Babbar Kotun Tarayya ranar Talat, 3 ga watan Fabrairu, 2026 bisa tuhuma guda biyar da hukumar ta shigar.
Dukkanin tuhume-tuhumen suna da da alaka da ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. Dukanninsu sun musanta laifuffukan da ake zargin su da aikatawa.
Malami ya fadi yadda ya samu dukiyarsa
A baya, kun samu labarin cewa tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya bayyana wa kotu hanyoyin da ya samu dukiyar da ake tuhumar ya tara.
Wannan ya faru ne a shari’arsa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ke yi masa a babban kotun tarayya a Abuja, inda ya ce duka ta halastacciyar hanya ya same su.
A ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairu, 2026, Malami ya shaida wa kotu cewa kadarorin da hukumar EFCC ke son kwace masa duk ya samu su ne ta hanya halaltattu kuma bisa doka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

