Sarki Sanusi II Ya Fadi Dalilan da Suka Sa ba zai Yi Shiru a kan Harkokin Gwamnati ba
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce sarakuna na gargajiya ginshiƙai ne wajen gina ƙasa da samar da jagoranci nagari
- Ya jaddada cewa ba ya buƙatar Kundin Tsarin Mulki don ba shugaban ƙasa ko gwamna shawara a matsayinsa na basarake
- Khalifan Tijjaniya, Sanusi II ya yi kira ga ƙara wakilcin mata a harkokin siyasa da kuma kawo ƙarshen tashin hankali a cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana muhimmancin sarakuna na gargajiya a matsayin ginshiƙai wajen gina ƙasa da jagoranci nagari.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne duk da sarakunan gargajiya ba su da rawar takawa da aka ware masu a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Source: Twitter
Sarki ya bayyana ra'ayinsa ne a wata hira da Channels Television Morning Brief ranar Laraba,4 ga watan Fabrairu, 2026.
Sarki Sanusi II ya fadi muhimmancin sarakuna
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ce ba ya buƙatar Kundin Tsarin Mulki don ba shugaban ƙasa ko gwamna shawara kan al’amuran ƙasa.
Ya ce yana da iko da damar bayar da shawara saboda mutane da al'ummar da ya ke jagoranta kuma suke kallonsa a matsayin shugabansu.
Sarkin ya ce:
“Shin ina buƙatar a gaya mini in ba shugaban ƙasa shawara? Shin ina buƙatar Kundin Tsarin Mulki ya ce idan na ga wani abu da ƙasa ke bukata, in je wurin shugaban ƙasa in ce, Mai girma Shugaban kasa, na ga wannan ba daidai ba ne?’ Ba na buƙatar Kundin Tsarin Mulki."
Ya kara da cewa sarakuna na gargajiya na da hakkin ba da shawara saboda shugabanci da suke da shi a kan al’umma, ba don tanadin kundin tsarin mulki ba.
Sarkin Kano na son a saka mata a siyasa
Sarkin ya kuma yi kira ga ƙarin wakilcin mata a harkokin siyasa, yana mai cewa mata na da rawar gani wajen tabbatar da jagoranci da shugabanci.
Ya ce akwai bukatar a samar da dama ga mata su kasance cikin mukamai kuma a zaɓe su domin inganta shugabanci mai wakilci sosai.

Source: Twitter
Sarki Muhammadu Sanusi ya kuma yi Allah wadai da tashin hankali da ake samu a gidaje, musamman inda wasu ke lakadawa matansu dukan kawo wuka.
Ya kara da cewa sarakuna na gargajiya suna da rawar gani wajen tabbatar da cewa ba a keta hakkin ɗan adam ba, kuma al’umma na buƙatar kula da masu rauni.
Sanusi II ya halarci taron sarakuna
A wani labarin, kun ji cewa Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, ya halarci wani muhimmin taro na musamman da ya haɗa sarakunan Afrika a birnin Lagos.

Kara karanta wannan
Tinubu ya sanar da matsaya kan janye cire tallafi da sauran manufofin tattalin arziki
Taron, wanda aka gudanar a ranar Litinin, 3 Fabrairu, 2026, a otal din Radisson Blu da ke Ikeja, ya haɗa manyan sarakuna da shugabannin gargajiya a Afirka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gidauniyar Ford Foundation, tare da UN Women da gwamnatin tarayya, ne suka shirya wannan taron.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

