Najeiya Ta Zama Abin Misali, An Fara Tattaunawa kan Sauye Sauyen Tinubu a Kasashen Duniya
- Bankin Duniya ya bayyana cewa shugabannin kasashe sun fara tattaunawa da daukar darasi daga sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya
- Daraktar Gudanar da Ayyuka ta Bankin Duniya, Anna Bjerde ta ce Najeriya ta zama abin misali a sassa daban-daban na duniya
- Ta yabwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa aiwatar da manufofin tattalin arziki a Najeirya, wanda ta ce sun fara haifar da 'da mai ido
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Bankin Duniya ya yaba da sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, inda ya bayyana Najeriya a matsayin abin koyi a duniya wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki.
Daraktar Gudanar da Ayyuka ta Bankin Duniya, Anna Bjerde, ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta jagoranci wata tawaga, suka gana da Shugaba Tinubu a Aso Rock, Abuja.

Kara karanta wannan
Tinubu ya sanar da matsaya kan janye cire tallafi da sauran manufofin tattalin arziki

Source: Twitter
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X yau Laraba, 4 ga watan Fabrairu, 2026.
Tsare-tsaren Tinubu sun ja hankalin duniya
Da take jawabi, Bjerde ta ce sakamakon gyare-gyaren da Najeriya ta samu cikin shekaru biyu da suka gabata abin yabawa ne sosai, kuma ana tattauna su a tsakanin shugabannin kasashen duniya, masu tsara manufofi da zuba jari.
Ta ce:
“Najeriya ta zama abin misali a tattaunawata a sassa daban-daban na duniya, domin sakamakon da aka samu cikin shekaru biyu abin yabawa ne matuƙa.”
Bankin Duniya ya yabawa Tinubu
Ta yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya tsaya tsayin daka wajen aiwatar da muhimman sauye-sauyen, tana mai cewa jajircewarsa ta ƙara gina kwarin gwiwa duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
“Duk da aiwatar da gyara yana da matukar wahala, amma ka dage ka ci gaba da tafiya a wannan hanya da ka dauko ba gudu babu ja da baya," in ji ta.
Bjerde ta ƙara da cewa bayanai daga kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya na nuna cewa sauye-sauyen suna haifar da sakamako mai kyau, tare da jawo masu zuba jari.
Najeriya za ta amfana da shirin Bankin Duniya
Dangane da sabon Tsarin Haɗin Gwiwa na Ƙasa da Bankin Duniya ke shiryawa, ta ce za a gina shi ne bisa burin Najeriya na gina tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya, da kuma samun ci gaba.
Ta jaddada cewa ƙirƙirar hanyoyin samar da ayyukan yi zai kasance a sahun gaba, musamman ganin yawan matasan Afirka da bukatar samar musu da ayyukan yi cikin gaggawa, cewar rahoton Premium Times.

Source: Twitter
Ta bayyana cewa Bankin Duniya zai ba da fifiko ga zuba jari a ababen more rayuwa, zamanantar da aikin noma da sauƙaƙa samun jari ga ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa.
Bola Tinubu ya kafe kan manufofinsa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa babu gudu, babu ja da baya a kan sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya.
Tinubu, wanda ya hau mulki a 2023 ya jaddada cewa Najeriya ta shiga yanayin da dole sai an yi gyara, saboda haka ba za yi wasa da aikin da aka ɗauko ba.
A cewar Tinubu, ko da yake matakan farko na gyare-gyaren tattalin arziki sun zo da raɗaɗi da wahala ga ‘yan ƙasa, amma hakan ba zai sa gwamnati ta fasa ba.
Asali: Legit.ng
