Bello Turji Ya Saki Tsohon Dan Bindiga Lankai, Ya Tara Jama'a Ya Yi jawabi
- Sakin dan bindiga Abdu Lankai da ake jagorantar yarjejeniyar zaman lafiya a Jibia a jihar Katsina, ya kawo sassauci ga fargabar barkewar rikici
- Mutanen Jibia sun ce tsawon kwanaki shida da ya ke tsare kasuwanni suna rufewa da wuri, zirga-zirga ta takaita, yayin da jama’a ke rayuwa cikin tsoro
- Komawar Lankai ya haifar da taruwar jama’a da tubabbun ‘yan fashi domin nuna goyon baya da komawa harkokin yau da kullum a karamar hukumar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Al’ummar Jibia sun yi murnar sakin Abdu Lankai, wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ya juya zuwa mai shiga tsakani, bayan kwashe kwanaki yana hannun yaran Bello Turji.
An bayyana cewa an kama Lankai ne bayan rikici da ya taso sakamakon gazawar wata mu’amalar sayar da makamai, lamarin da ya girgiza yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a yankin.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa sakinsa ya dawo da kwanciyar hankali, inda jama’a suka ce barazanar tashin hankali ta ragu, kasuwanci ya fara dawowa,
Halin da aka shiga bayan kama Lankai
A tsawon kwanaki shida da kama dan bindiga Lankai, mazauna Jibia sun ce sun yi rayuwa cikin fargabar abin da ka iya biyo baya.
Legit ta rahoto cewa an bayyana cewa kasuwanni sun rika rufewa da wuri, hanyoyi sun yi shiru, jama'a kuma na kwana cikin fargaba kai musu hari da dare.
Wani mazaunin garin ya ce a wancan lokacin ba wanda ke kwana cikin kwanciyar hankali, saboda tsoron cewa duk wani abu da ya samu Lankai zai rushe tsarin zaman lafiyar da aka yi da ƙyar.
Rawar da Lankai ya taka wajen sulhu
Ko da yake a baya an san Lankai da fashi da garkuwa da mutane, mazauna Jibia sun ce a baya-bayan nan ya zama jigo wajen sulhunta ƙungiyoyin 'yan bindiga da al’umma.

Source: Facebook
An ce ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta Jibia, warware sabani, hana kai hare-hare kan ƙauyuka, da kuma shawo kan mayaka su bar tashin hankali.
'Dan bindiga Lankai ya tara jama'a
Sakin Lankai ya zo da annashuwa a Jibia, daruruwan jama’a sun taru a yankin Malamawa domin murna, suna siffanta lamarin da alamar samun sauki.
Wasu rahotanni sun nuna cewa kimanin tubabbun ‘yan bindiga 300 masu biyayya ga Lankai sun halarci taron domin nuna goyon baya.
Da yake magana bayan sakinsa, Lankai ya gode wa Allah da ya tsira, ya kuma yi kira ga kowa da kowa da ya rungumi zaman lafiya, yana mai cewa abin da ya faru ya bar wa Allah.
Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa yaran Bello Turji ne suka saki Lankai kuma ya koma gida lafiya.
'Yan ta'adda sun yi sabon kwamanda
A wani labarin, mun kawo muku cewa kingiyar 'yan ta'ddan ISWAP a jihar Borno ta zabi sabon kwamanda da zai jagoranci ayyukanta.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun zabi wani da ake kira Abu Khalifa ya cigaba da jagorantar ta'addancin da suke yi.
Hakan na zuwa ne bayan sojojin Najeriya sun kashe kwamandan kungiyar mai suna Julaibib a wani farmaki da suka kai musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


