Kwamitin Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Duba Watan Ramadan 2026

Kwamitin Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Duba Watan Ramadan 2026

  • Kwamitin ganin jinjirin wata na kasa a Nijeriya ya ce yana bin ka’idojin Shari’ar Musulunci wajen duba wata, kuma ba zai sauya su da fasahar zamani ba
  • Wani mamba a kwamitin ya bayyana cewa fasahar zamani na taimako ne kawai wajen tantance duba wata, amma ba ta maye gurbin gani da ido
  • An yi kira ga 'yan kasa su bi sanarwar Mai Alfarma Sarkin Musulmi domin tabbatar da hadin kai da kauce wa rarrabuwar kawuna wajen ganin wata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, FCT – Kwamitin ganin jinjirin wata na kasa a Nijeriya ya sake jaddada matsayinsa kan muhimmancin ganin wata da ido wajen tantance farko da karshen watannin Musulunci.

Mamba a Kwamitin Ganin Jinjirin Wata na Kasa, Simwal Usman Jibril ya ce duk da cigaban fasahar zamani, har yanzu ba a samu wata sahihiyar hujja ta Shari’a da ta amince da maye gurbin gani da ido gaba daya ba.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

Ami alfarma Sarkin Musulmi na Najeriya
Mai alfarma Sarkin Musulmi a hagu, wata a gefen dama. Hoto: HQ Nigerian Army|Getty Images
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Muslim News ta yi da shi shi a ranar Talata, 3, Fabrairu, 2026, inda ya yi bayani dalla-dalla kan tsarin da Najeriya ke bi wajen ganin wata.

Tsarin Shari’a kan duba jinjirin wata

Simwal ya ce matsayar da manyan malamai karkashin Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci suka dauka ya ginu ne a kan hadisin da ke umartar Musulmi da su fara azumi bisa ganin jinjirin wata da ido, ko kuma cika kwanaki 30.

Ya ambato hadisin da ke cikin Sahih Muslim mai lamba 1081, wanda ke cewa a yi azumi idan an ga wata, a kuma ajiye azumi idan an sake ganinsa, amma idan gajimare ya rufe sama, a cika kwanaki 30.

A cewarsa, mafi yawan malamai sun fahimci wannan umarni a matsayin gani da ido kai tsaye, ba wai dogaro da lissafin taurari kawai ba.

Rawar fasaha wajen ganin wata

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda aka tsara harbe ministan tsaro, Janar Christopher Musa

Simwal ya ce a halin yanzu babu wata fatawa daga kwamitin malamai da aka amince da ita a Najeriya da ke halatta amfani da lissafi ko na’urori na zamani su kadai wajen tabbatar da ganin wata.

Saboda haka, ya ce ana amfani da fasaha ne kawai domin taimakawa wajen tantance yiwuwar ganin wata, ba wai daukarta a matsayin hujja ta karshe ba.

Ya kara da cewa ana gudanar da aikin ganin wata a dukkan watannin Hijira 12, ba a watan Ramadan kadai ba idan za a fara azumi.

An bukaci hadin kai a Ramadan

Baya ga haka, Simwal ya jaddada cewa hadin kan Musulmi abu ne mai matukar muhimmanci a harkokin ibada na bai daya kamar azumi

Ya ce a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ne jagoran da Shari’a ta amince da shi wajen sanar da ganin wata.

A cewarsa, bin wannan tsari na taimakawa wajen hana rikice-rikice a tsakanin al’umma, tare da tabbatar da tsari da kwanciyar hankali a ibadu irin su azumi da bukukuwan Idi.

Simwal Usman Jibril da ke kwamitin duba gani wata.
Dan kwamitin ganin wata a Najeriya, Simwal Usman Jibril. Hoto: @Simwal
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, Simwal ya yi kira ga Musulmi da su girmama shugabanci da malamai, su kuma kauce wa duk wani abu da zai iya haddasa rarrabuwar kawuna.

Kara karanta wannan

An 'gano' wanda Ganduje ya yi zargin ya tona masa asiri game da badakala a Kano

An shiga watan Sha'aban a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya fitar da sanarwa bayan duba watan Sha'aban.

A sanarwar da ya fitar, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya bayyana cewa ranar Talata, 20, Janairu, 2026 ce ranar farko ta watan Sha’aban 1447.

An sanar da shiga sabon watan ne bayan Sarkin Musulmi ya umarci dukkan 'yan kasa su fita duba wata a lokacin da Rajab ya zo karshe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng