Tsohon Shugaban NIMASA a Mulkin Buhari Ya Shiga Hannun ICPC

Tsohon Shugaban NIMASA a Mulkin Buhari Ya Shiga Hannun ICPC

  • Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta tsare tsohon Shugaban NIMASA, Bashir Jamoh, bisa zargin cin zarafin ofis
  • Majiyoyi sun ce an kama shi ne bayan ya yi watsi da da dukkanin gayyatar da aka dade ana yi masa zuwa ofishin ICPC
  • Hukumar ICPC ta tabbatar da kamen, amma ba ta fayyace cikakken zargin da ake yi wa tsohon Shugaban ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar ICPC mai yaki da rashawa ta kasa ta ICPC ta tsare tsohon Shugaban hukumar kula da harkokin ruwa da tsaron teku ta Najeriya (NIMASA), Bashir Jamoh.

Kara karanta wannan

An biyo kan masu shara: Gwamna ya yi barazanar korarsu kan rijistar zama yan APC

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Jamoh, wanda ya shugabanci NIMASA daga shekarar 2020 zuwa 2023, yana hannun ICPC har zuwa daren jiya a lokacin da ake hada wannan rahoto.

ICPC ta kama tsohon Shugaban NIMASA
Dr. Bashir Aliyu,Shugaban (tsakiya), Shugaban ICPC na Najeriya Hoto: ICPC Nigeria
Source: Facebook

Majiyoyin sun shaida wa Daily Trust cewa an bayyana cewa hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan tsohon shugaban NIMASA ya kasa amsa gayyatar da aka rika tura masa, duk da yawan korafe-korafen da aka shigar kansa.

Zargin da ake yi wa tsohon Shugaban NIMASA

Wani daga cikin majiyoyin ya ce daya daga cikin korafe-korafen da aka mika wa ICPC na zargin Jamoh da bai wa kansa fifiko ba bisa ka’ida ba.

Ta bayyana cewa ana zargin ya rika saye da sayarwa na bogi, lamarin da aka bayyana a matsayin cin zarafin mukami da cin amana.

Majiyar ta ce:

“ICPC ta kama shi ne bayan ya kasa amsa gayyatar da aka yi masa sau da dama. Ana bincikensa ne kan zargin cin zarafin ofis a lokacin da yake Shugaban NIMASA.”

ICPC ta tabbatar da kDa aka tuntubi kakakin hukumar ICPC, John Odey, ya tabbatar da kama Jamoh, sai dai ya ki yin karin bayani kan takamaiman zarge-zargen da ake masa.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro zai rikide zuwa siyasa bayan gwamnatin APC ta ba shi mukami

Ya ce zai sake tuntubar manema labarai da zarar ya samu cikakken bayani kan dalilin kamen.

Yadda Jamoh ya jagoranci NIMASA

NIMASA hukuma ce ta gwamnati da ke da alhakin kula da harkokin teku a Najeriya, tare da tsara dokoki da manufofi da ke inganta harkokin sufuri da kasuwanci ta ruwa.

Hukumar na da alhakin tabbatar da tsaro da lafiyar jiragen ruwa, bunkasa harkokin teku, kare muhalli na ruwa, da kuma tabbatar da bin dokoki da ka’idojin harkokin teku.

ICPC ta tabbatar da tsare Jimoh, amma ta ki karin bayani
Ginin ofisoshin ICPC a Najeriya Hoto: ICPC Nigeria
Source: Twitter

A shekarar 2021, Bashir Jamoh ya rubuta wasika kai tsaye zuwa Hukumar EFCC inda ya bukaci a binciki zargin badakalar Naira tiriliyan 1.5 da aka danganta da shi.

Wannan ya biyo bayan zargin da wani mai suna Jackson Ude ya yi, inda ya ce Jamoh ya karkatar da N1.5trn zuwa asusun kansa, tare da wani karin zargin karkatar da dala miliyan 9.5 zuwa wani asusu da aka danganta da shi.

An nada sabon Shugaban NIMASA

A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin Dayo Mobereola a matsayin sabon darakta-janar na Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Dalilan da suka jawo Buhari ya kori Hadiza Bala Usman duk da kusancinsu

Wannan naɗi ya nuna wani sabon mataki a ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta harkokin sufurin ruwa, tsaro a teku a faɗin ƙasar.

Naɗin Mobereola ya biyo bayan karewar wa’adin Bashir Jamoh, wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 4 ga watan Maris, 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng