Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya yi wasu sabbin nade nade a hukumar NPA, NIMASA

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya yi wasu sabbin nade nade a hukumar NPA, NIMASA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabbin mambobi a hukumomin gudanarwa na hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA da hukumar da kula da hanyoyi ruwan Najeriya, NIMASA.

Babban sakataren ma’aikatar sufuri, Sabiu Zakari ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja, inda yace shugaban kasa ya nada Honorabul Asita a matsayin shugaban hukumar gudanarar NIMASA.

KU KARANTA: Sunusi ya baiwa Ganduje sa’o’i 24 ya sake shi, ko kuma ya dauki mataki a kansa

A ranar Talata, 10 ga watan Maris ne shugaban hukumar NIMASA, Dakuku Peterside ya yi murabus biyo bayan karewar wa’adinsa na shekaru hudu, inda ya mika ragamar jan hukumar ga sabon shugabanta, Bashir Jamoh.

Sauran yan hukumar gudanarwar NIMASA da shugaba Buhari ya amince da nadinsu sun hada da: Victor Ochei, babban daraktan dakon kaya; Chudi Offordile, babban darakta kudi da mulki, Shehu Ahmed babban daraktan aikace aikace, Adekola Adefemi, Muhammed Abubakar da Hassan Mahmud.

Haka zalika shugaba Buhari ya nada Akin Ricketts a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NPA, sauran mambobin hukumar sun hada da: Muhammed Koko, babban darakta; Prof. Idris Abdulkadir, babban darakta da Onari Brown, shi ma babban darakta, Ghazali Muhammed, John Akpanuoedehe, Binta Masi Garba, Mustapha Dutse da Abdulwahab Adeshina.

Sai dai sanarwar ta tabbatar da kasancewar Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar hukumar NPA. Sanawar ta karkare da cewa a ranar 20 ga watan Maris ne ministan sufuri, Rotimi Amaechi zai rantsar da su.

A wani labarin kuma, shugabar NPA, Hadiza Bala ta bayyana cewa ita fa buduwar gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai bace, kuma ba karuwanci ta yi ta samu wannan mukami da take kai ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel