Halin da Iyalan Mafarauta 16 da Aka Kashe a Edo Suke Ciki, Sun Magantu kan Diyya
- Iyalan Hausawa 16 da aka kashe a Edo sun ce har yanzu suna cikin jimami da kunci, ba tare da samun wani taimako daga gwamnati ba
- Shugaban mafarauta, Malam Ibrahim Isa, ya koka kan yadda gwamnati da shugabanni suka yi shiru, duk da alkawuran da aka yi
- Wani mai kare haƙƙin ’yan Arewa ya ce za su shirya zanga-zanga a Abuja, tare da barazanar katse kai kayan abinci zuwa Edo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Iyalan Hausawa 16 da aka yi wa kisan gilla a jihar Edo sun yi magana game da halin da suke ciki bayan watanni 10.
Mutanen suka ce har yanzu suna cikin jimamin rashin yan uwansu da aka hallaka ba tare da samun wani taimako ba daga gwamnati.

Source: Twitter
Kisan gilla: Iyalan mafarauta 16 sun koka
Hakan na cikin wani bidiyo da DCL Hausa ta zanta da yan uwan mamatan wanda ta wallafa a shafin Facebook a jiya Talata 3 ga watan Faburairun 2026.
A cikin bidiyon, jagoran mafarautan, Malam Ibrahim Isa ya nuna damuwa game da halin ko in kula da aka nuna game da abin da ya faru.
Ya bayyana damuwa kan halin da iyalan mamatan ke ciki na halin kunci da maraici duba da cewa mafi yawa ba su da manyan yara.
Ya ce:
"Ban da ku yan jaridu, daga gwamnatin Kano da yan siyasa ko masarauta babu wanda ya zo ya tuntube mu wata 10 kenan da kwana 16.
"Mai Martaba Sarkin Rano Allah ya saka masa da alheri mun ziyarce shi har sau shida yana fada mana cewa za a kai kuka wurin gwamnati za ta saurare mu.
"Karshe ma yana daga cikin kwamitin da aka kafa, Gwamna ya tura su Edo aka yi sati daya, biyu ba mu ji komai ba, sai muka ce za mu je mu yi wa Sarki barka da zuwa.
"Ya tambaye mu har yanzu ba a yi muku komai ba? muka ce eh, amma bai ce mana ga yadda aka yi a can ba, kuma hakika ya je."

Kara karanta wannan
Abin da aka tanadar wa iyalan sojojin da suka yi yunkurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki

Source: Twitter
Kisan gilla: An shirya gagarumar zanga-zanga
Malam Ibrahim ya ce su dai ba su san inda suka dosa ba saboda har yanzu ba su san makomar iyalan mamatan ba da yan uwansu.
"Har zuwa yau babu wanda ya zo ya tambaya me yake faruwa bayan watanni da kisan wadannan yara a Edo."
- Ibrahim Isa
Wani mai kare hakin yan Arewa, Kwamred Kabiru Sani Garko ya ce a ranar 11 ga watan Faburairun 2026 sun raba takardu za su fito zanga-zanga kan lamarin a Abuja.
Ya ce idan ba a dauki mataki ba, za su hana kai kayan abinci jihar Edo domin nuna bacin ransu game da abin da ya faru.
Wasu yan Edo sun farmaki Hausawa
Mun ba ku labarin cewa fusatattun matasa sun kori Hausawa a kasuwar dabbobi ta Ekpoma, inda suka yanka awaki sakamakon zanga-zanga.
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kira da a kwantar da hankali domin kauce wa ramuwar gayya.
’Yan sanda sun ce an kama mutane da dama da ake zargin suna da hannu a lamarin da ya faru wanda ya jawo maganganu a kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
