Magana Ta Girma: Amurka Ta Turo Karin Wasu Sojoji Wata 1 bayan Hari a Najeriya
- Amurka ta aiko da wasu rukunin sojoji zuwa Najeriya, domin ƙara haɗin gwiwa wajen yaƙar ta’addanci a kasashen Yammacin Afirka
- Majiyoyi suka ce matakin ya biyo bayan yarjejeniya tsakanin kasashen biyu cewa ana buƙatar ƙarin matakai kan barazanar ’yan ta’adda
- Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin, tana musanta zargin cin zarafin Kiristoci, tana cewa kowa na shan wahala daga matsalar tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Amurka ta sanar da aike da ƙaramin rukunin sojoji zuwa Najeriya a kokarin ci gaba da yaki da ta'addanci.
Amurka ta tabbatar da turo sojojin ne a kokarin hadin guiwa da Najeriya domin kakkabe yan ta'adda da suke addabar al'umma.

Source: Getty Images
Kasar Amurka ta turo sojoji Najeriya
Rahoton Reuters Africa ya ce babban janar mai kula da rundunar sojin Amurka a Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin R.M. Anderson, ya tabbatar da haka a ranar Talata 3 ga watan Faburairun 2026.
Janar Anderson ya shaida cewa an yanke shawarar tura sojojin ne bayan Najeriya da Amurka suka amince cewa akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen yaƙar barazanar ta’addanci a yankin Yammacin Afirka.
A cewarsa:
“Wannan yarjejeniya ta haifar da ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashenmu, ciki har da tura wani ƙaramin rukunin sojojin Amurka da ke da kwarewa na musamman daga Amurka.”
Sai dai Janar Anderson bai bayyana cikakken adadin sojojin ba ko girman aikin da za su yi a Najeriya.

Source: Facebook
Martanin Najeriya kan zuwan sojoji Najeriya
Rahoto ya nuna cewa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar da cewa wani rukuni na sojoji na nan a Najeriya, amma shi ma bai bayar da ƙarin bayani ba.
Wannan ci gaba shi ne karo na farko da aka amince da shi cewa sojojin Amurka na aiki a ƙasar tun bayan hare-haren sama da Amurka ta kai kan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya a ranar Kirsimeti, 2025.
Rahoto ya kuma nuna cewa Amurka na gudanar da jiragen sa ido a sararin samaniyar Najeriya daga Ghana tun ƙarshen watan Nuwambar 2025, cewar AP News.

Kara karanta wannan
APC na tilasta wa ma'aikatan gwamnati shiga jam'iyyar? An samu gaskiya kan rade radin
Wani tsohon jami’in Amurka ya ce rukunin sojojin da aka tura na da hannu sosai wajen tattara bayanan sirri da kuma taimaka wa sojojin Najeriya kai hari kan ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ta’addanci.
A halin da ake ciki, Najeriya na fuskantar matsin lamba daga Washington, bayan Shugaba Donald Trump ya zargi ƙasar da gazawa wajen kare Kiristoci daga ’yan ta’adda da ke aiki a Arewa maso Yamma.
'Dan majalisar Amurka ya gana da gwamnan Plateau
Mun ba ku rahoton cewa 'dan majalisar Amurka da ke yada zargin kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya, ya gana da Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang.
Riley Moore ya bayyana muhimmancin aiki tare tsakanin Najeriya da Amurka domin kare rayukan Kiristocin da ake zargin ana muzgunawa.
Ganawar tasu dai na zuwa ne yayin da Najeriya da Amurka suka yi hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci a fadin kasar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
