'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10, Sun Kona Gidaje a Sabon Harin da Suka Kai Kwara

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10, Sun Kona Gidaje a Sabon Harin da Suka Kai Kwara

  • 'Yan bindiga sun kashe mazauna garuruwan Woro da Nuku tare da kona gidaje da dama a karamar hukumar Kaiama dake jihar Kwara
  • Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya yi Allah-wadai da harin inda ya umarci jami'an tsaro su tsananta sintiri don dakile wasu hare haren
  • Mazauna wadannan garuruwa sun bayyana cewa har yanzu akwai fargaba a zukatunsu game da yiwuwar dawowar 'yan ta'addar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - 'Yan bindiga sun kaddamar da mummunan hari a garuruwan Woro da Nuku dake ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara.

A yammacin ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2025 ne aka ce maharan suka farmaki garuruwan, inda suka kashe aƙalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.

'Yan bindiga sun farmaki garuruwa 2 a jihar Kwara
Taswirar jihar Kwara, inda 'yan bindiga suka kashe akalla mutane 10 a harin da suka kai. Hoto; Legit.ng
Source: Original

Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa 'yan bindigar sun fito ne daga dajin Borgu dake maƙwabtaka da Jihar Neja domin kai wannan harin.

Kara karanta wannan

An biyo kan masu shara: Gwamna ya yi barazanar korarsu kan rijistar zama yan APC

'Yan bindiga sun kai hari jihar Kwara

Maharan sun shigo garuruwan ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi domin tsorata jama'a.

Mazauna yankin sun shiga cikin mawuyacin hali yayin da iyalai da dama suka rasa masoyansu a cikin wannan mummunan harin na bazata.

Baya ga kisan kai, maharan sun kona gidaje da dama, lamarin da ya sa mutane da yawa rasa matsugunansu, kamar yadda rahoton ya nuna.

Wani shugaban al'umma ya bayyana cewa har yanzu ana neman wasu mutanen da suka tsere zuwa daji domin tsira da rayuwarsu.

Martanin gwamnatin jihar Kwara

Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana matuƙar jimami da alhini game da wannan kisan kiyashi da aka yi wa mazauna garuruwan Kaiama.

A cikin wata sanarwa, Mai magana da yawun gwamnan jihar, Rafiu Ajakaye, ya ce Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq yana bibiyar halin da ake ciki a koda yaushe.

A cewar gwamnatin, maharan suna ƙoƙarin karkata hankalin jami'an tsaro ne daga nasarorin da ake samu wajen kakkabe sansanonin masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An shiga firgici a Gombe, 'yan bindiga sun farmaki garuruwa 4, sun kashe mutane

Gwamna Abdulrazaq ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalai da dukkan al'ummar Kaiama, inda ya tabbatar musu cewa ba za a tsaurara matakai sosai.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kai Kwara
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya na jawabi ga 'yan jarida, jihar Kwara. Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

Halin da ake ciki bayan harin 'yan bindiga

An umurci dakarun tsaro da su ƙarfafa sintiri da ayyukan kakkabe ƴan ta'adda domin hana sake faruwar irin wannan danyen aikin a jihar, in ji rahoton Punch.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ƴan sandan jihar ba ta fito da takamaiman bayani kan yawan jami'an da aka tura ba.

To sai dai mazauna yankin sun bayyana cewa har yanzu akwai fargaba a zukatunsu game da yiwuwar dawowar maharan domin sake farmakarsu.

A halin yanzu, ana ci gaba da jimamin waɗanda suka rasa rayukansu yayin da aka fara jana'izar wasu daga cikin mamatan a ƙauyukansu.

'Yan bindiga sun farmaki jihar Gombe

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe wata mata mai juna biyu da dan uwanta sannan suka sace wasu mutane a harin da suka kai jihar Gombe.

Rahoton ya nuna cewa 'yan bindiga sun fara matsawa garuruwan Gombe da kai hare-hare da sace mutane, duk da kokarin da jami'an tsaro ke yi.

Shugabannin al'umma sun nemi gwamnati ta tura karin jami'an tsaro domin dakile ayyukan ta'addanci dake neman addabar yankunan jihasr Gombe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com