Abin da Emefiele Ya Ce ga Buhari a Takardar Neman Izinin Sauya Fasalin Naira

Abin da Emefiele Ya Ce ga Buhari a Takardar Neman Izinin Sauya Fasalin Naira

  • Wani shaida a kotu ta bayyana cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya rubuta takarda domin neman amincewa kan sake fasalin kudi
  • A cewar shaidar da EFCC ta gabatar, marigayi Muhammadu Buhari ya amince da shirin ne da sharadin a rika buga sababbin kudin a cikin gida
  • Hukumar EFCC ta zargi Emefiele da karya dokar CBN, yayin da lauyoyinsa ke jaddada cewa shugaban kasa na lokacin ya amince da hakan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani mai bada shaida ya bayyana a kotu game da tuhumar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da ake yi.

Shaidan ya bayyana cewa Emefiele ya rubuta wata takarda zuwa ga tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, domin neman amincewarsa kan sake fasalin Naira a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, Gwamnatin Tinubu ta rufe bakin matasan N Power

An tabbatar Buhari ya amince wa Emefiele kan sauya fasalin Naira
Marigayi Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Chinedu Eneaya, jami’in bincike a Hukumar EFCC, ya bayar da wannan shaida a gaban Babbar Kotu da ke Abuja, cewar Premium Times.

Yayin ba da bahasi, mutumin ya kasance a matsayin shaida ta bakwai a shari’ar da ake yi wa Emefiele kan zargin sake fasalin Naira ba bisa ka’ida ba.

Tuhume-tuhume da ke kan Godwin Emefiele

Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume guda hudu, ciki har da sake fasalin Naira ba bisa ka’ida ba, saba wa umarnin doka, da kuma aikata abin da ya jawo illa ga jama’a.

EFCC ta ce Emefiele ya karya sashe na 19 na dokar CBN, wanda ya tanadi cewa ba za a iya sauya kudin kasa ba sai da amincewar shugaban kasa bisa shawarar kwamitin gudanarwar bankin.

Sai dai Emefiele ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa an gabatar da takardar neman izini ga Shugaba Buhari kafin aiwatar da shirin.

A zaman kotun, lauyan Emefiele, Olalekan Ojo (SAN), ya bukaci shaidan EFCC ya karanta wani bangare na takardar da aka aika wa Buhari, wadda ta bayyana cewa sake fasalin kudin ya zama dole domin magance karuwar kudin bogi da karancin kudaden da ke da inganci.

Kara karanta wannan

Malami ya sanar da kotu hanyoyin da ya samu kudadensa a shari'arsa da EFCC

Shaidan ya kuma amince cewa shirin ya kunshi dakile boye kudade da jama’a ke yi, duk da haka, ba a bayyana ranar da aka rubuta takardar ba a zaman kotun.

Don tabbatar da cewa Buhari ya amince da shirin, lauyan ya bukaci shaidan ya karanta rubutaccen amincewar shugaban kasar, inda ya ce:

“An amince, amma a tabbatar da an samar da kudin a cikin gida.”
Rawar da Buhari ya taka a sauya fasalin Naira
Marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammdu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Facebook

Kamfanonin da suka buga takardun Naira

Shaidan ya shaida wa kotu cewa kamfanin De La Rue na Birtaniya ne ya tsara zanen kudin, yayin da Kamfanin Buga Kudi na Najeriya (NSPM) ya dauki nauyin buga kudaden.

Ya ce dukkanin kamfanonin sun bi umarnin shugaban kasa, kuma an biya su hakkokinsu gaba daya, cewar Vanguard.

Sai dai shaidan ya ce bai iya tuna ko EFCC ta yi amfani da ka’idojin cikin gida na CBN ba, amma ya jaddada cewa binciken nasu ya gudana ne bisa dokar CBN.

Alkalin kotu, Mai Shari’a Maryanne Anenih, ta amince da bukatar lauyan Emefiele na gabatar da rahoton binciken EFCC “domin adalci,” tare da dage sauraron shari’ar zuwa 10 ga Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

A baya, wasu shaidu sun bayyana cewa kwamitin gudanarwar CBN bai taba ba da shawarar sake fasalin kudin ga Buhari ba kafin sanar da aiwatar da shirin a 2022.

Ana zargin Emefiele da cire $6.23m a CBN

An ji cewa shaida na 11 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke gabatarwa a kan shari'a da tsohon Gwamnan EFCC ya fito da jawaban boye.

Ya bayyana yadda aka ce an fitar da Dala miliyan 6.23 daga babban bankin kasa na CBN da takardun bogi a zamanin Emefiele.

Shaidan ya ce an cire kudin ne a reshen Garki na CBN da ke Abuja domin ayyukan masu sa ido kan zabe da harkokin gudanar da zaben.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.