Bayanai Sun Fito game da Kawancen Sojin Najeriya da Amurka
- Ana ci gaba da batu a kan yarjejeniyar da Najeriya ta shiga da Amurka game da zargin cewa ana kashe kiristoci da gayya a kasar Afrikar
- Tun bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya a cikin kasashe da ake da damuwa a kansu, kasar nan ke kai gwauro, tana kai mari
- Tuni aka shiga yarjejeniya iri-iri tsakanin Najeriya da Amurka, daga ciki har da sama wa sojin wurin zuba mai a jiragen yaki marasa mayuka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Bayanai sun fara fitowa a kan haɗin gwiwar soja tsakanin Najeriya da Amurka, tun bayan da Shugaban kasar, Donald Trump ya jefa ta a cikin kasashen da ake da damuwa a kansu.
Kasar Amurka da wasu 'yan majalisar tarayyarta sun bayyana cewa ana yi wa kiristocin Najeriya kisan kare dangi da gangan.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya ɗauki wannan mataki ne a watan Oktoba na shekarar 2025.
A watan Nuwamba na 2025, Trump ya yi barazanar tura sojoji zuwa Najeriya domin kawar da ’yan ta’addan da yake zargin suna kashe Kiristoci.
An samu bayanai kan yarjejeniyar Amurka da Najeriya
Wata majiya ta bayyana wa jaridar The Cable cewa Amurka ta buƙaci kafa wuri a Najeriya domin ba wa jiragen yakinsa marasa matuka damar zuba mai bayan sun dawo daga Ghana.
Majiyar ta ce tattaunawa ta yi nisa, kuma an zaɓi wata jiha a Arewa maso Gabas saboda a can ne ake gudanar da ayyukan amfani da jirage marasa matuka a Najeriya.
Majiyar ta ce an ƙi zaɓen Legas ko Abuja saboda dalilai na tsaro, amma magana ta yi nisa a kan amfani da jihar ta Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
A ranar Talata, shugaban rundunar Amurka da ke kula da Afrika, (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson, ya bayyana cewa Amurka ta tura ƙaramar tawagar sojoji zuwa Najeriya.
Wannan sanarwa ta janyo ce-ce-ku-ce, kasancewar ita ce karon farko da aka amince da kasancewar sojojin Amurka a ƙasar tun bayan harin Kirsimeti.
Ana aikin tsaro tsakanin Najeriya da Amurka
Sai dai wata majiyar ta tabbatar da cewa wannan aiki tsakanin Amurka da Najeriya ba sabon abu ba ne, amma ann fadada aikin.
Daga cikin ayyukan da ake sa ran sojojin za su yi akwai ba da shawara, horo da taimako da bayanan sirri, ba shiga yaƙi kai tsaye ba.
A baya, Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya tabbatar da cewa sojojin Amurkan ba na yaƙi ba ne, illa masu tallafa wa horo da tattara bayanai.
An yi gargadi kan shigo da soji Najeriya
Wani masani a bangaren sanin laifuffuka Dr. Suleiman Isyaku Muhammad jami’ar Dutse ya shaida wa Legit cewa barin sojojin waje a kasar nan ba zai haifar da da mai ido ba.
Ya bayyana cewa Amurka ta nuna shirinta na aiki tare da sojojin Najeriya a ƙarƙashin tsarin AFRICOM.
Dr. Suleiman Isyaku Muhammad ya ƙara da cewa jami’an Amurka na ganin haɗin gwiwar za ta iya taimakawa wajen magance matsalar tsaro.
Ya ce:
“Wannan shiga muhibbar kasa ne. A matsayin Najeriya na kasa mai ’yancin, tana da nata manufofin tsaro.”
Ya kawo misalai daga wasu ƙasashe daga ciki har da Afghanistan, Iraq, Mali da Philippines, inda ya ce shigar sojojin ƙasashen waje ya ƙara tsananta matsalolin tsaro.
Ya shawarci Najeriya da a bi a hankali wajen barin sojoji su shigo ƙasar nan kai tsaye ta ci gaba da aiki a kasar nan.
Sojojin Amurka sun dura Fadar Shugaban ƙasa
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata tawagar sojojin Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock.
Tawagar ta Amurka ta zo ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afrika (USAFRICOM), Janar Dagvin R. Anderson, tare da wwasu jami’ai.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya tarbi Janar Dagvin Anderson tare da babban jami'i a ofishin jakadancin Amurka a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


