Yadda Buhari Ya Kafa Tarihin zuwa Kasashe 21 a 2016 yayin da Tinubu Ya Je 24 a Mulkinsa

Yadda Buhari Ya Kafa Tarihin zuwa Kasashe 21 a 2016 yayin da Tinubu Ya Je 24 a Mulkinsa

Shugaba Bola Tinubu ya yi tafiye-tafiye ƙasashen waje 10 kacal a 2025, yayin da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ninka shi a shekara daya.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tafiye-tafiye da shugabanni a Najeriya ke yi zuwa kasashen ketare na ci gaba da jawo magana a kasa.

An bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tafiye-tafiye ƙasashen waje 10 a shekarar 2025 wanda ake ganin ya yi yawa.

Yawan tafiye-tafiyen Buhari da na Tinubu a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Muhammadu Buhari yayin barin Najeriya a cikin jirgi. Hoto: Muhammadu Buhari, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tarihin da Muhammadu Buhari ya kafa a 2016

Sai dai wani rahoton Ledership ya ce marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tafiye-tafye zuwa kasashe 21 a shekarar 2016 kacal.

Bulaguron da ya yi a 2016 ita ce shekarar da ya fi yawan fita ƙasashen waje a tsawon mulkinsa na shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Shaidar EFCC ta yi bayani kan alakar Yahaya Bello da zargin almundahar N80bn

Wannan kwatancen ya sake tasowa ne a yayin da ake ci gaba da muhawara kan yawan tafiye-tafiyen shugabannin ƙasa, kuɗin da ake kashewa, da kuma amfaninsu.

Wasu kasashe da Tinubu ya ziyarta a 2025

Rahotanni daga fadar shugaban ƙasa sun nuna cewa tafiye-tafiyen Tinubu a 2025 sun bazu ne tsawon watanni takwas, galibi kuma sun shafi taron ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ziyarar aiki, da tarurrukan jawo hannun jari.

A watan Janairu, Tinubu ya yi tafiye-tafiye uku, ya fara ne da tafiya Ghana domin halartar rantsar da sabon shugaban ƙasar, John Dramani Mahama.

Daga nan ya wuce Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sannan ya ƙare watan da ziyara zuwa Tanzania, inda ya halarci taron 'Mission 300 Africa Energy Summit' a birnin Dares Salaam.

A watan Fabrairu, Shugaban ya yi tafiya zuwa Faransa a wata ziyara ta aiki mai zaman kansa, kafin ya wuce Habasha domin halartar taron shugabannin ƙasashen Afirka na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a Addis Ababa.

A watan Afrilu, Tinubu ya sake komawa Turai, inda ya shafe lokaci a Faransa da Birtaniya, yana gudanar da tattaunawa da jami’ai da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanar da matsaya kan janye cire tallafi da sauran manufofin tattalin arziki

A watan Mayu, Shugaban ya kai ziyara Italiya, inda ya halarci bikin nadin Paparoma Leo XIV a Vatican, taron da ya samu halartar shugabannin ƙasashe da dama na duniya.

Buhari ya fi Tinubu yawan ziyara kasashe a mulkinsa
Shugaba Bola Tinubu yayin da yake barin Najeriya zuwa Faransa. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Sauran tafiye-tafiye da Tinubu ya yi

A ƙarshen watan Yuni zuwa farkon Yuli, Tinubu ya yi tafiya zuwa Saint Lucia a matsayin ziyarar ƙasa, wacce ita ce ziyara ta farko da shugaban Najeriya ya kai ƙasar Caribbean, kafin daga nan ya wuce Brazil.

A watan Agusta, Shugaban ya tafi Japan domin halartar taron ci gaba ta (TICAD), sannan daga nan ya sake komawa Brazil don tattaunawar zuba jari da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa.

A watan Satumba, Tinubu ya yi hutun aiki na kwanaki 10, wanda ya raba tsakanin Faransa da Birtaniya.

Ziyarar ƙarshe ta Tinubu a 2025 ta gudana ne a watan Disamba, inda ya tafi Turai domin hutun ƙarshen shekara, gabanin taron da aka yi a Abu Dhabi da aka shirya gudanarwa a Janairu 2026.

Bulaguron Tinubu a Janairun 2026

Daily Trust ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shafe kwanaki 22 a wajen Najeriya a cikin watan Janairun 2026 kaɗai, kamar yadda wani nazari kan tafiye-tafiyensa na ƙasashen waje da aka sanar a hukumance ya nuna.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban ƙasa ta kashe N34bn a kan canjin kuɗi don tafiye tafiyen Tinubu

A cikin wannan lokaci, shugaban ƙasar ya kai ziyara Faransa, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma Jamhuriyar Türkiye (Turkiyya).

Jerin kasashen da Tinubu ya je a mulkinsa

Gaba ɗaya, tafiye-tafiyen Tinubu sun ratsa Afirka, Turai, Asiya, Caribbean da Kudancin Amurka, tare da mai da hankali kan diflomasiyyar tattalin arziki, tattaunawar sauyin yanayi, haɗin gwiwar yankuna da hulɗar kasashe.

1. Turkiya

2. Faransa

3. Jamus

4. The Netherlands

5. Birtaniya

6. Vatican

7. Jamhuriyar Benin

8. Chadi

9. Ghana

10. Senegal

11. Guinea

12. Equatorial Guinea

13. Kenya

14. Habasha

15. Afirka ta Kudu

16. Tanzania

17. Saudiyya

18. Qatar

19. UAE

20. Brazil

21. Saint Lucia

22. Amurka

23. Indiya

24. China

Yadda Buhari ya keta hazo mafi yawa a shekarar 2016
Marigayi Muhammadu Buhari yayin da yyake sauka daga jirgi bayan dawowa Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Tafiye-tafiyen Buhari da suka zama daban

A gefe guda kuma, shekarar 2016 ta kasance shekarar da aka fi samun yawan tafiye-tafiye da wani shugaban Najeriya ya taba yi, inda Muhammadu Buhari ya kai ziyara ƙasashen waje sau 21.

A shekarar, tafiye-tafiyen Buhari sun ratsa kusan dukkan watanni, kuma sun ta’allaka ne kan kalubalen tsaro, durkushewar tattalin arziki, yaƙi da cin hanci da rashawa, da tarurrukan ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan

Gambari: Halin da Buhari ya shiga a kan dagulewar tsaron Najeriya

A watan Janairu 2016, Buhari ya ziyarci Kenya da Jamhuriyar Benin, a Fabrairu kuma ya kai ziyara Faransa, Saudiyya, Qatar da Birtaniya.

Tsakanin Maris da Afrilu, ya tafi Amurka, China da Equatorial Guinea, a watan Mayu, ya koma Birtaniya domin halartar taron yaƙi da cin hanci da rashawa, cewar Punch.

A watan Agusta, Buhari ya sake komawa Kenya sannan ya wuce Chadi don halartar rantsar da shugaban ƙasa, a Satumba, ya halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a Amurka.

Sauran tafiye-tafiyen sun haɗa da Jamus a Oktoba, Morocco a Nuwamba sannan ya ziyarci Senegal da Gambia a matsayin taron sulhun ECOWAS, kafin ya koma Birtaniya.

Rahoton ya nuna cewa wasu daga cikin tafiye-tafiyen Buhari a 2016 sun shafi jinyar lafiya a London, lamarin da ya taimaka wajen yawaitar adadin tafiyarsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An kwatanta tafiye-tafiyen Buhari a shekara 1 da na Tinubu
Marigayi Muhammadu Buhari yana shafa addu'a a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Facebook

'Amfanin tafiye-tafiyen ga tattalin arziki'

Wasu na ganin tafiye-tafiyen na da matuƙar muhimmanci wajen jawo zuba jari, ƙarfafa diflomasiyya da haɗin gwiwar tsaro a yankuna, yayin da masu suka ke ci gaba da tambayar kuɗin da ake kashewa da tasirinsu a cikin gida.

Kara karanta wannan

Bayan shigowar Abba, Ganduje ya faɗi dacen da aka yi na samun Tinubu a Najeriya

Sai dai idan aka duba ƙididdiga kawai, tafiye-tafiyen Buhari 21 a 2016 sun kasance abin da ba kasafai ake gani ba.

Peter Obi ya soki yawan tafiye-tafiyen Tinubu

Kun ji cewa Peter Obi ya soki tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Tinubu ke yi zuwa kasashen waje inda ya ce ya kwashe kwanaki akalla 196 a waje.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023 ya nuna takaicinsa kan yadda Tinubu ke yawo a kasashen waje alhalin Najeriya na cikin "wani hali".

Ya ce rashin jawabin sabuwar shekara da shiru kan matsalolin tsaro na nuna rashin kishin talakawa da gazawar gwamnatin Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.