Binciken Yunkurin Juyin Mulki Ya Sa An Kama Tsohon Janar Mai Rike da Sarauta
- Hukumomin tsaro sun kara fadada bincike kan yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda aka kama wani tsohon Janar
- Rahotanni sun nuna cewa ana zargin tsohon Janar din da alaka ta kusa da wanda ake zargi a matsayin jagoran yunkurin, duk da rashin shaidar kai-tsaye
- Hakan na zuwa ne bayan rundunar tsaro ta tabbatar da yunkurin juyin mulki bayan karyata batun a wata sanarwa da ta fitar a shekarar 2025 da ta wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun kara tsaurara matakan bincike kan mutanen da ake zargi da hannu a yunkurin juyin-mulki da ake cewa an shirya domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan na zuwa ne yayin da jerin wadanda ake zargi ke kara tsawaita, ciki har da wani tsohon babban hafsan soja a rundunar tsaro ta kasa.

Source: Facebook
Rahoton The Sun ya tabbatar da cewa wani tsohon Janar mai rike da sarauta, Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya, ya fada hannun jami’an tsaro.
Dalilin kama tsohon Janar
Wata majiya ta soji ta bayyana cewa an kama tsohon Janar Mohammed Ibrahim Gana ne sakamakon dadaddiyar alakar da ke tsakaninsa da Kanar Alhassan Ma’aji, wanda ake zargi a matsayin babban jagoran shirin juyin-mulkin.
Majiyar ta ce ana zargin tsohon Janar din ya taimaka wa Ma’aji wajen samun shiga Kwalejin Tsaro ta Najeriya a watan Agusta, 1995, lamarin da ya sanya masu bincike ke zargin cewa yana iya kasancewa da masaniya kan shirin.
Sai dai majiyar ta jaddada cewa babu wata hujja kai-tsaye da aka samu da ke danganta tsohon Janar da aiwatar da shirin, face dai alakar da ke tsakaninsa da wanda ake zargi a matsayin jagora.
Baya ga jami’an soja, rahotanni sun nuna cewa an kama wasu fararen hula da dama da ake zargi da taimaka wa wadanda ke cikin shirin.

Source: Facebook
Rahotanni sun ce wadanda aka tsare sun fito ne daga jihohi da dama na Arewa da kuma Abuja, ciki har da Niger, Katsina, Kaduna, Plateau, Kano, Gombe, Bauchi, Kebbi, Jigawa, Zamfara, Taraba, Yobe, Kogi, Sokoto da Adamawa.
A jerin mutum 40 da Premium Times ta fitar, ta wallafa cewa cikin wadanda aka kama akwai Laftanar Kanal Ibrahim Gana da wasu rahotanni ke zargin cewa da ne ga tsohon Janar din da aka rike ne.
Martanin Ministan tsaro, Janar Musa
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa da yunkurin juyin mulki ya yi nasara, shi ma yana cikin wadanda za su shiga matsala.
Ya ce an tsara cewa idan ya ki mika wuya, za a harbe shi, amma ya bayyana masu shirin a matsayin mutanen da ba su fahimci karfin rundunar sojin Najeriya ba.
Janar Musa mai ritaya ya kara da cewa ko da sojoji ba su yi martani ba, ‘yan Najeriya za su tashi tsaye domin hana dawowar mulkin soja a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

