Shettima Ya Bude Sabon Shirin Tallafa wa Matasa Miliyan 10 a Harkar Kudi
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da sabon shirin horaswa kyauta a fadin kasa domin ba ’yan Najeriya miliyan 10 ilimin hada-hadar kudi
- Shirin na karkashin ofishin Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ta hannun kwamitin PreCEFI, tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi
- Rahotanni sun nuna cewa an tsara shirin ne domin bai wa mata da matasa kwarewa a harkar kudi, zuba jari da dabarun habaka tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, FCT – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani babban shirin horaswa kyauta da ke da nufin ba ’yan kasa miliyan 10 ilimi a harkar kudi da fahimtar yadda ake tafiyar da kudi yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa ofishin mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar shirin ta hannun kwamitin shugaban kasa kan tattalin arziki, PreCEFI da Kashim Shettima ke jagoranta.

Source: Facebook
Shettima ya wallafa a X cewa manufar shirin ita ce karfafa wa ’yan Najeriya, musamman mata da matasa, gwiwa da kwarewa a bangaren ilimin kudi, dabarun zuba jari da sauransu.
Shirin da Kashim Shettima ya kaddamar
Shettima ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta da kungiyoyin kwararru guda shida domin tsara manhajar horaswa, hanyoyin bayar da shaidar kwarewa, dabarun koyon fasahar zamani da kuma tsarin jagoranci da tallafawa mahalarta shirin.
Punch ta rahoto cewa an bayyana cewa hadin gwiwar za ta taimaka wajen karfafa harkokin kudi da kasuwanci a dukkan jihohin Najeriya.
Kungiyoyin da suka shiga yarjejeniyar sun hada da Institute of Chartered Accountants of Nigeria, Chartered Institute of Bankers of Nigeria, Chartered Institute of Stockbrokers da National Institute of Credit Administration.
Wadannan kungiyoyi sun kware a harkokin aikin banki, ilmin akanta, saye da saida hannun jari, cin bashi da makamantansu.
Bayanai sun nuna cewa sauran su ne Chartered Risk Management Institute da Nigerian Institute of Innovation and Entrepreneurship.
Jawabin Kashim Shettima kan shirin
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa sanya hannu kan yarjejeniya ya bude muhimmiyar hanyar karfafa dan Adam.
Shettima ya ce Najeriya ba za ta iya cin gajiyar yawan matasanta ba sai an tanadi kwarewa da nagartaccen tarbiyya da suka dace da tattalin arziki da ke da alaka da fasahar zamani da ke kara habaka.

Source: Facebook
Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta kafa sahihin tsari da zai hada kwarewar wadannan kungiyoyi domin bunkasa shigar da jama’a harkar kudi ta hanyar horaswa, wayar da kai, karfafa matasa da kuma tallafa wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i.
Matasa miliyan 10 za su amfana
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa dole ne shirin ya bai wa mata da matasa fifiko, domin su ne ginshikin bunkasar tattalin arzikin kasa nan gaba.
Ya kuma sanar da kaddamar da horaswar kyauta ga ’yan Najeriya miliyan 10, inda mata da matasa za su kasance a sahun gaba a dukkan sassan kasar nan.
Shettima ya ziyarci Tudun Biri
A wani labarin, mun kawo muku cewa Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ziyarci yankin Tudun Biri a jihar Kaduna.
Tare da rakiyar gwamnan Kaduna, Uba Sani, Kashim Shettima ya kaddamar da gidaje sama da 100 da gwamnati ta gina wa mutanen yankin.
Lamarin ya biyo bayan bama-bamai da jirgin sojin Najeriya ya sake a garin yayin da jama'a ke bikin Maulidi, inda gwamnati ta musu alkawura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


