Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Sabon Kwamanda da zai Gwabza da Sojojin Najeriya
- Kungiyar ISWAP ta sanar da nada Abu Khalifa a matsayin sabon kwamandanta a yankin Timbuktu Triangle bayan kashe tsohon kwamanda, Julaibib
- Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe Julaibib ne a yankin Kimba da ke karamar hukumar Damboa ta Jihar Borno yayin wani farmaki
- Duk da sabon nadin, har yanzu kungiyar ba ta bayyana mataimakin kwamanda a hukumance ba, sai dai ana ta rade-radi kan yiwuwar nada Tuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Kungiyar ISWAP ta sake fasalin jagorancinta a yankin Timbuktu Triangle bayan mutuwar daya daga cikin manyan kwamandodinta, Julaibib.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun ce 'yan ta'addan sun dauki wannan mataki ne domin cike gibin jagoranci da ya biyo bayan nasarar sojoji a kansu.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an nada Abu Khalifa a matsayin sabon kwamanda ne bayan tattaunawa da shawarwari a tsakanin shugabannin ISWAP.
Kisan Julaibib ya faru ne yayin wani sumame da dakarun Operation Hadin Kai suka kai a yankin Kimba da ke Damboa, lamarin da ya tilasta wa kungiyar daukar matakin gaggawa.
Kungiyar ISWAP ta yi sabon kwamanda
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa bayan kawar da Julaibib, shugabannin ISWAP sun fahimci bukatar gaggauta nada sabon kwamanda domin kauce wa rudani a cikin kungiyar.
A cewar rahoton Daily Post, wannan ya sa aka gudanar da tattaunawar cikin gida kafin amincewa da sunan Abu Khalifa a matsayin sabon jagoransu.
A cewar bayanan sirri, an dade ana ganin Abu Khalifa a matsayin daya daga cikin manyan jagorori masu tasiri a yankin Timbuktu Triangle.

Source: Twitter
An kashe kwamandan ISWAP
Rahotanni sun nuna cewa Julaibib ya rasa ransa ne a yayin wani farmaki da sojojin Najeriya suka kai a karkashin Operation Hadin Kai. An ce an kai harin ne bayan samun bayanan sirri kan motsin mayakan a yankin Kimba.
Kashe Julaibib ya kasance babban rashi ga ISWAP, kasancewarsa daya daga cikin kwamandojin da ke taka rawar gani wajen jagorantar hare-hare da shirye-shiryen tsaro na kungiyar a yankin.
Batun mataimakin kwamanda
Duk da nada Abu Khalifa a matsayin sabon kwamanda, majiyoyin sun ce ISWAP ba ta kai ga bayyana mataimakin kwamanda a hukumance ba. Wannan ya bar gibi a tsarin jagoranci, duk da cewa suna ta tattaunawa a tsakanin mayakan.
Rahotanni sun nuna cewa wani mai suna Tuja na daga cikin wadanda ake ganin za su iya zama mataimakin kwamanda. Sai dai, har zuwa yanzu, babu wata sanarwa ta karshe da ta tabbatar da wannan nadin.
Wannan sauyin jagoranci na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ISWAP da Boko Haram a yankunan Kudancin Borno.
An kashe 'yan ta'adda a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun gwabza fada da 'yan ta'adda da dama a wata karamar hukuma a jihar Zamfara.
Rundunar soji ta sanar da cewa ta kai harin ne bayan samun bayanai da suka nuna cewa sama da 'ya ta'adda 100 sun taru a cikin daji.
Yayin gwabza fada da aka yi, sojoji sun kashe shugaban 'yan bindiga a yankin, Gwaska Dan Karami tare da kone sansaninsa baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


