Gambari: Halin da Buhari Ya Shiga a kan Dagulewar Tsaron Najeriya
- Tsohon Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari ya bayyana halin da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya faɗa a kan tsaro
- Gambari ya bayyana cewa duk da ana samun nasara a yaƙi da yan ta'addan Boko Haram, an kuma samu ɓullar ƴan ta'addan daji
- Farfesa Ibrahim Gambari ya ƙaryata rahotannin barazanar juyin mulki a ƙarshen mulkin marigayi Buhari gabanin zaben 2023
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya yi magana kan yadda aka ji da rashin tsaro a lokacin.
Ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya shiga damuwa sosai saboda rashin nasarar da bai samu ba wajen magance dukkannin matsalolin tsaro a Najeriya kafin ya bar mulki.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Abin da Buhari ya gayawa gwamnonin Arewa kan 'dan takararsa a zaben 2023

Source: Facebook
Gambari ya yi wannan bayani ne a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu, 2026.
Buhari ya damu kan tsaro - Gambari
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Muhammadu Buhari ya kan samu kwanciyar hankali idan ya tuna irin nasarorin da aka samu wajen dakile Boko Haram a gwamnatinsa.
Ya ce abin kan yi masa daɗi musamman ganin cewa babu wani yanki na ƙasar da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar a lokacin da ya bar mulkin Najeriya.
Sai dai hakan bai hana shi ci gaba da damuwa kan sauran matsalolin tsaro da suka saka yan Najeriya a gaba a lokacin da ya ke shugabanci ba.

Source: Facebook
Gambari ya ce:
“Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi damunsa shi ne rashin ikon magance rashin tsaro kafin ya bar mulki. Ya yi abubuwa da dama, daga ciki har da tabbatar da cewa babu wani yanki na Najeriya da Boko Haram ke riƙe da shi.”

Kara karanta wannan
Tsohon Minista ya yi bayanai, ya fadi abin da ya hana Buhari magance rashin tsaro da cin hanci
Rashin tsaron da ya fi damun Buhari
Sai dai ya ƙara da cewa hare-haren ‘yan fashi da makami da rikice-rikicen da ke faruwa a Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya sun ci gaba da damun Buhari ƙwarai.
Ya ce:
“Halin da ake ciki a Arewa maso Yamma, da Arewa ta Tsakiya, har da ‘yan bindiga, yana masa zafi matuƙa. Ya kan ce ya yi duk abin da zai iya domin mutanen nan."
Gambari ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa an samu barazanar juyin mulki a ƙarshen mulkin Buhari. Ya ce a matsayinsa na Shugaban Ma’aikata, ba a taɓa gabatar masa da irin wannan rahoto na cewa akwai barazanar kifar da gwamnatinsa ba. Ya ƙara da cewa Buhari, duk da kasancewarsa tsohon shugaban soja kuma daga bisani zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ya kiyaye kusanci da rundunar soji ne cikin iyakokin kundin tsarin mulki.
Kan salon jagorancinsa, Gambari ya ce Buhari mutum ne mai kyautatawa ga waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa ta siyasa da ta kai.
Sakon Buhari ga gwamnoni gabanin zaben 2023
A baya, mun wallafa cewa tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin ya yi bayani dalla-dalla kan matsayin Buhari game da zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Gambari ya ce marigayi Buhari bai yi imani da ɗora ko zaɓar wanda zai gaje shi ba kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, yana mai cewa ya bar al’amarin a hannun jam’iyya da ‘yan ƙasa.
A cewarsa, Buhari bai taɓa nuna wa kowa cewa yana da ɗan takara da ya fi so ba, duk da cewa manyan jiga-jigan gwamnatinsa sun shiga takarar shugaban ƙasa a wancan lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
