Takaitaccen tarihin Ibrahim Gambari, wanda ya maye gurbin Abba Kyari a fadar shugaban kasa
Daga karshe bayan walankeluwa tare da kauce kauce, fadar shugaban kasa ta sanar da Alhaji Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Ibrahim Gambari shi ne wanda zai maye gurbin marigayi Abba Kyari a matsayin babban maigadin ofishin shugaban kasa da fadar Aso Rock Villa gaba daya.
A yayin zaman majalisar zartarwa na ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da Gambari, don haka muka kawo muku wasu bayanai game da shi:
KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya za ta sallami yan Najeriya 11,000 saboda Coronavirus
- Cikakken sunansa Ibrahim Agboola Gambari
- An haife shi a ranar 12 ga watan Nuwambar 1944, shekarunsa 75
- Dan asalin jahar Kwara ne, daga dangin Sarkin Ilorin, Sulu Gambari
- Ya taba zama ministan kasashen waje a gwamnatin Soja ta Buhari 1984-1975
- Ya yi karatun sakandari a makarantar King’s College Legas
- Ya yi karatun digiri a a bangaren Economics a London School of Economics, 1968
- Ya yi digiri na biyu a 1970, digiri na uku 1974 a jami’ar Columbia, New York, USA, a bangaren kimiyyar siyasa
- Ya fara koyarwa a shekarar 1969 a jami’ar City University of New York
- Ya koyar a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, Kaduna
- A shekarar 1986-1989 ya koyar a jami’o;in Johns Hopkins School of Advanced International Studies, Georgetown University and Howard University.
- Ya koyar tare da gudanar da bincike bincike a Brookings Institution
- Gwamnatin tarayya ta karrama shi da lambar girmamawa na CFR
- Ya zama mataimakin shugaban majalisar dinkin duniya Banki-Moon a shekarar 2010
- A yanzu haka shi ne mashawarcin shugaban majalisar dinkin duniya a kan hadin kan kasashe game da Iraq
- Ya taba zama mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya a shekarar 2005
- Shi ne uban jami’ar jahar Kwara daga shekarar 2013 zuwa yanzu.
- Ya wakilci sakataren majalisar dinkin duniya a Angola, 2002-2003
- Tun daga shekarar 2000-2012 yake wakiltar Najeriya a majalisar dinkin duniya
- Ya shigaban kwamitin majalisar dinkin duniya dake yaki da wariyar launin fata a Afirka ta kudu, 1990-1994
- Daga 1990-1999 shi ne wakilin Najeriya na dindindin a majalisar dinkin duniya
- Ibrahim Gambari yana da mata, yara da jikoki da dama
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng