Hajji: An Yi Wa Gwamna da Matansa 2 Gwajin Lafiyar da Saudiyya Ta Wajabta, Sakamako Ya Fito
- Likitoci sun yi wa Gwamna Nasir Idris da matansa biyu gwajin lafiyar da Saudiyya ta wajabta ga duk wanda zai tafi aikin Hajjin 2026
- Rahotanni sun nuna cewa sakamakon gwajin ya nuna Gwamna Nasir da matansa suna cikin koshin lafiyar da za ta ba su damar zuwa Hajjin bana
- Gwamna Idris ya yabawa shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Kebbi bisa namijin kokarin da yake wajen tafiyar da harkokin Hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince an yi masa gwajim lafiya, wanda kasar Saudiyya ta wajabtawa duk wani musulmi da ke niyyar zuwa Hajjin 2026.
Gwamnan ya kammala gwajin lafiyar cikin nasara tare da samun shaidar cewa yana cikin koshin lafiya da zai ba shi damar gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Source: Twitter
Gwaje-gwajen da aka yi wa Gwamna Nasir
Leadership ta rahoto cewa gwajin lafiyar ya haɗa da binciken dakin gwaje-gwaje da kuma duban jiki gaba ɗaya, wanda aka gudanar bisa umarnin hukumomin lafiya na Saudiyya da kuma Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).
A cewar umarnin, duk wani maniyyaci da ke shirin zuwa aikin Hajji dole ne ya fuskanci gwajin lafiya domin tabbatar da cewa ba ya ɗauke da wata cuta da Saudiyya ta haramta shiga da ita yayin aikin Hajji.
An gudanar da gwajin lafiyar gwamnan ne a fadar gwamnati da ke Birnin Kebbi a daren Lahadi, tare da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi (PWA), Faruk Aliyu Yaro Enabo.
Gwamnan Kebbi ya yabawa shugaban PWA
Da yake jawabi a taƙaice, Gwamna Nasir Idris ya yaba wa shugaban hukumar PWA bisa nagartaccen shugabanci da ƙwarewarsa a harkokin aikin Hajji.
Ya bayyana cewa zaɓensa a matsayin shugaban hukumar jin dadin alhazai ya taimaka matuƙa wajen nasarar aikin Hajji a jihar Kebbi.
Gwamnan ya kuma umarci ƙungiyar likitocin da ke aikin gwaje-gwajen lafiya da su kasance masu jajircewa da gaskiya, tare da tabbatar da cewa an tantance dukkan maniyyata kafin a ba su damar tafiya aikin Hajji.
An yi wa matan gwamnan Kebbi gwajin lafiya
Haka zalika, matan gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasare da Hajiya Nafisa Nasir Idris, sun kammala gwajin lafiyar da aka tanada domin aikin Hajjin 2026.
An yi musu gwajin ne ta hanyar binciken dakin gwaje-gwaje da kuma duban lafiyar jiki a fadar gwamnati da ke Birnin Kebbi.

Source: Facebook
Matan gwamnan sun yaba wa shugaban hukumar PWA bisa yadda yake tafiyar da harkokin Hajji cikin nasara a duk shekara, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Sun kuma yaba wa mijinsu, Gwamna Nasir Idris, bisa cikakken goyon bayan da yake bai wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai, musamman yadda gwamnatinsa ke biyan kuɗin Hadaya ga dukkan maniyyatan Kebbi tun daga hawansa mulki.
Gwamnatin Kebbi ta nemi karin kujerun Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kebbi ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 10 domin samun karin kujeru 1,300 na Hajjin 2026 ga ‘yan jihar.
Shugaban hukumar jin dadin alhazar ta Kebbi, Alhaji Faruku Aliyu Yaro ya shaidawa manema labarai a Birnin Kebbi cewa rancen ya taimaka wajen cike gibin kujerun da ake bukata.
Ya kara da cewa wannan mataki ya taimaka wajen kare dukkanin kujerun da aka ba wa jihar, kuma babu maniyyacin da zai rasa kujerarsa ta bana.
Asali: Legit.ng


