Yan Ta'adda Sun Bi Sawun Dan Kasuwar Kano, Sun Ɗauke Shi a Jihar Nassarawa

Yan Ta'adda Sun Bi Sawun Dan Kasuwar Kano, Sun Ɗauke Shi a Jihar Nassarawa

  • Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun dauke wani attajirin kasuwa daga Kano a jihar Nasarawa
  • Tuni ‘yan sanda suka fara aikin bincike tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai domin a kai ga gano inda ya kai shi
  • Rahotanni sun bayyana yadda yan ta'addan suka cimma ɗan kasuwan, sannan suka yi cikin dawa da shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano –Wani shahararren dan kasuwa dan asalin jihar Kano, Alhaji Rabiu Salisu, ya fada hannun masu garkuwa da mutane.

Wasu ƴan ta'adda da ba a kai ga gano su ba sun sace shi a kauyen Rukubi da ke karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa.

An sace wani attajirin Kano a Nassarawa
Kayode Egbetokun, Sufeton yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa lamarin ya faru ne yayin da yake tafiya daga kauyen, inda yan ta'adda suka tare shi, aka yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun dimauce bayan fashewar abu mai kama da bam

'Yan ta'adda sun sace attajirin Kano

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ƴan sandan Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin da ya faru ranar Juma’a.

A cewar rahoton, ƴan sandan sun samu rahoto da karfe 4.30 na yamma daga wani ma’aikacin kamfanin Olam da ke Rukubi, mai suna Murtala Abubakar.

Rahoton ya jawo hankalin jami’an tsaro, inda aka ce an dauki mataki cikin gaggawa domin dakile lamarin da kuma ceto wanda aka sace.

Yadda aka yi garkuwa da attajirin Bakanon

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa Alhaji Rabiu Salisu, wanda dan kasuwa ne daga Kano, yana kan hanyarsa ta dawowa ne daga Rukubi lokacin da maharan suka afka masa.

Rahotannin sun ce miyagun mutanen sun yi anfani da karfi da barazana kafin su yi awon gaba da shi zuwa cikin dazuka da ke kewaye da yankin.

An sace attajiri a wani kauye da ke jihar Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa inda aka sace attajirin Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

A lokacin da rahoton ya isa ofishin ‘yan sanda, jami’in rundunar a yankin Ekye ya dauki matakin tura tawaga ta musamman zuwa wurin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Minista ya dauko da zafi, ya fara shirin garkame ma'aikatan Abuja a gidan yari

Wannan tawaga ta hada da jami’an ‘yan sanda da kuma ‘yan sa-kai na yankin, domin bincike da kokarin bin sahun maharan.

Majiyoyin sun ce:

Da muka samu rahoton, baturen ƴan sanda ya tattara jami’ai tare da hadin gwiwar ‘yan banga domin zuwa wurin."

Sanarwar ta kara da cewa an rika binciken dazuzzuka da kewaye domin gano inda aka kai wanda aka sace.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin bincike domin ceto wadanda aka sace ba tare da bata lokaci ba

Haka kuma ta ce ana kokarin kamo wadanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci bisa doka.

Satar waya: Matasan Kano sun fusata

A baya, kun ji cewa wasu matasa sun fusata da aka kama wani matashi da laifin yunkurin satar wayar salula daga hannun wata baiwar Allah a Kano.

Rahotanni sun nuna cewa matasa sun banka wa matashin da ake zargi da satar waya wuta a unguwar Dorayi karshen waya da ke jihar a ranar Asabar, 31 ga watan Fabarairu, 2026.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an ƴan sanda sun yi nasarar zuwa wajen, amma ko da suka isa rai ya riga ya yi halinsa sakamakon bugu da ƙuna da matashin ya sha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng