Malami Ya Dauki Mataki na Hana EFCC Kwace Kadarori 57 da Ya Mallaka a Abuja, Kano

Malami Ya Dauki Mataki na Hana EFCC Kwace Kadarori 57 da Ya Mallaka a Abuja, Kano

  • Abubakar Malami ya bukaci kotu ta soke umarnin kwace kadarorinsa 57 yana mai cewa ya ayyana su a hukumar CCB lokacin yana mulki
  • Tsohon babban lauyan ya bayyana cewa wasu daga cikin gidajen gado ne da mahaifinsa ya bari, kuma EFCC ta boye wa kotu gaskiya
  • A halin yanzu, ana jiran ganin matakin da kotun za ta dauka a kuma martanin da EFCC za ta yi kan wannan sabon yunkuri na Malami

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja da ta soke umarnin kwace kadarorinsa.

Malami ya bukaci kotun ta janye dukkan takunkumin da aka sanya wa kadarorinsa 57 wadanda hukumar EFCC ke zargin na haram ne.

Abubakar Malami ya roki kotu t hana EFCC kwace kadarorinsa 57
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a da ke fuskantar tuhuma daga EFCC. Hoto: @aamalamiSAN, @officialEFCC
Source: Twitter

Wannan bukata na zuwa ne bayan da Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi a ranar 6 ga Janairu, 2026, in ji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Zargin lalata da matar aure: Magidanci ya sassara wani mutum da adda har lahira

Malami ya damu kan wasu kadarori 3

Malami, ta bakin lauyoyinsa karkashin Joseph Daudu (SAN), ya fi mayar da hankali kan wasu kadarori uku dake lamba 9, 18, da 48 a jerin kadarorin da aka kwace.

Ya bayyana cewa ya dade yana ayyana wadannan kadarori a hukumar da'ar ma'aikata (CCB), wanda ya fara tun daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Kadarorin sun hada da wani fili a Nasarawa GRA dake Kano da kuma wani katafaren gidansa a Wuse II dake birnin Abuja, kamar yadda rahoton ya nuna.

Tsohon ministan ya bayyana cewa ya sayi gidan Abuja ne a kan naira miliyan 150, sannan ya sayi wani ginin gidauniyar Kadi Malami a kan naira miliyan 56.

Malami ya tabo batun gidan gado

Game da kadara ta 48, Malami ya ce yana rike da ita ne a matsayin amana ga iyalan mahaifinsa, Kadi Malami da ya rasu, in ji rahoton jaridar The Guardian.

Lauyoyinsa sun yi ikirarin cewa EFCC ta samu umarnin kotun ne ta hanyar boye wasu muhimman hujjoji da kuma bayar da bayanan karya.

Kara karanta wannan

Tofa: Gwamna ya rufe dukkan makarantu, ya sanya dokar zaman gida ta awanni 20

Sun bayyana cewa tsarin aikin EFCC ya ci zarafin hakkin Malami na mallakar dukiya da kuma zaman lafiya tare da iyalinsa.

A cewar lauyan, Malami ya bayyana dukkan hanyoyin samun kudin shigar sa wadanda suka kai naira miliyan 374 daga albashi da sauran alawus-alawus.

Abubakar Malami ya zargi EFCC da boye gaskiya da kuma kawo batutuwan karya gaban kotu don kwace kadarorinsa.
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a a kotu, lokacin da EFCC ta gurfanar da shi. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Martanin kotu da na EFCC

Wadannan kadarori dai na biliyoyin nairori ne kuma an karkasa su a jihohin Abuja, Kebbi, Kano, da kuma Kaduna.

Malami ya bukaci kotun da ta hana EFCC kara tsoma baki cikin kadarorin sa ko kuma damun iyalinsa yayin gudanar da bincike.

A halin yanzu, ana jiran ganin matakin da kotun za ta dauka kan wannan sabon yunkuri na tsohon babban lauyan kasar.

DSS na binciken makamai a gidan Malami

A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar DSS ta fara bincike kan tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, bayan rahoton gano makamai a gidansa.

Jami’an hukumar EFCC ne aka ce sun gano makaman a lokacin da suke binciken gidan Malami a karkashin binciken zargin laifuffukan kudi da ake yi masa.

Sai dai saboda mallakar makamai ba ta cikin hurumin EFCC, an ce hukumar ta mika dukkan makaman da aka gano ga DSS domin ci gaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com