An Ji Yadda Sheikh Rigi Rigi Ya Rasu a Gadon Asibiti da Wasiyyar da Ya Bar Wa Musulmai

An Ji Yadda Sheikh Rigi Rigi Ya Rasu a Gadon Asibiti da Wasiyyar da Ya Bar Wa Musulmai

  • Iyalan marigayi Sheikh Usman Rigi-Rigi sun bayyana wasiyyar da malamin yake yawan maimaita wa kafin Allah ya masa rasuwa
  • A daren ranar Lahadi, 1 ga watan Fabrairu, 2026 ne Allah Ya karbi ran Sheikh Khalifa Usman Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi a asibitin 44
  • Daya daga cikin matan marigayin ta bukaci masoyansa a cikin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba da su yi hakuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaria, Nigeria - A safiyar yau Litinin ne aka samu labarin rasuwar sanannen malamin addinin musulunci da ke garin Zaria a jihar Kaduna, Sheikh Khalifa Usman Kusfa, wanda aka fi sani da Sheikh Rigi-Rigi.

Kara karanta wannan

Zargin lalata da matar aure: Magidanci ya sassara wani mutum da adda har lahira

Iyalan shehun malamin sun tabbatar da cewa Sheikh Rigi-Rigi ya dade yana jinya kafin Allah SWT ya karbi ransa a daren jiya Lahadi, 1 ga watan Fabrairu, 2026.

Sheikh Usman Kusfa.
Sheikh Usman Kusfa Rigi-Rigi a wurin karatu a masallacinsa da ke Zaria Hoto: Madinatu Yarwa
Source: Facebook

A wata hira da RFI Hausa ta yi da daya daga cikin matan marigayin, ta ce malamin ya dade yana jinya a tsaye, kafin daga bisani ciwo ya ci karfinsa har aka kwantar da shi a asibitin 44 da ke Kaduna.

Yadda Sheikh Rigi-Rigi ya rasu a asibitin 44

Matar Sheikh Rigi-Rigi ta bayyana cewa shehun malamin ya shafe sama da kwana 40 yana kwance a asibiti, kafin ya cika a daren ranar Lahadi.

"Ya shekara daya da rabi yana ciwo amma a tsaye, bai yarda ya kwanta ba har sai lokacin da Allah ya yi, aka kwantar da shi a asibiti. An kai shi asibitin 44, a nan ya samu wajen kwana 40, a cikin kwana na 40 ne Allah ya yi ikon Shi.
"Ba na tare da shi, dukkanmu muna gida, mu hudu matansa muna gida tare da 'ya'yanmu duk muna gida, sai muridan shi ne can su ke tare da shi (a asibiti) tare da babban dansa.

Kara karanta wannan

An sanya lokacin jana'izar Sheikh Usman Rigi Rigi, 'masoyin Annabi ya rasu'

"Muna yawan waya da shi, ni na yi magana da shi, muryarsa ba ta canza ba komai na shi bai canza ba, ya kan kira mu a waya mu hadu tare da yara duka mu yi magana amma komai na shi bai canza ba kamar lafiyarsa kalau," in ji ta.

Wasiyyar da malamin ya bar wa musulmi

Ta kuma bayyana wasiyyoyin da yake yawan fadaqa iyalansa da sauran musulmai a wurin wa'azinsa da sauran karatuttukan da ya saba yi.

"Kullum maganarsa kenan a rike Allah, a rike Manzon Allah (SAW), a rike zumunci, a bi shehunnai, a rike darikar Tijjaniyya, a hada kan iyali, kullum maganarsa kenan har Allah ya yi hukuncinsa," In ji matar Sheikh Rigi-Rigi.

A karshe, ta bayyana cewa Shehu yana da masoya da yawa a cikin Tijjaniya da ma wadanda ba musulmi ba, ta roki kowa da ya yi hakuri domin mutuwa tana kan kowa.

Sheikh Rigi-Rigi.
Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Khalifa Usman Kusfa Rigi-rigi Hoto: Sheikh Waddu Media
Source: Facebook

An sa lokacin jana'izar Sheikh Rigi-Rigi

Kuna da labarin cewa iyalai da muridan Sheikh Usman Kusfa Rigi-Rigi sun sanya lokacin da za a gudanar da jana'izar malamin, wanda ya rasu jiya Lahadi.

An ce za a gudanar da sallar jana'izar marigayin a Kusfa da ke Zaria a yau Litinin, inda ake sa ran dubun-dubatar musulmi za su halarci sallah da birne shi.

Malam Abubakar Danyaro, wanda ya kasance surukin Sheikh Rigi Rigi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce za a yi jana'izar bayan sallar La'asar, a kofar gidansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262