Gudaji Kazaure: "Da Ina Majalisa, Da Sai Na Kawo Ƙudurin Tsige Tinubu"

Gudaji Kazaure: "Da Ina Majalisa, Da Sai Na Kawo Ƙudurin Tsige Tinubu"

  • Tsohon dan majalisar wakilan Najeriya, Hon Gudaji Kazaure ya bayyana takaicinsa kan yadda Majalisar Wakilai ke tafiya a yanzu
  • Ya ce majalisa ta gaza tsayawa tsayin daka wajen kare hakkin talakawa idan ta lura cewa gwamnatin tarayya ta tafka wasu kura-kurai
  • Tsohon dan majalisar ya ce da yana zuren majalisa har yanzum zai kalubalanci bashin tiriliyoyin Naira da dokokin haraji domin a gyara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa – Tsohon dan majalisar Jigawa, Hon Gudaji Kazaure ya bayyana takaici a kan yadda ake gudanar da majalisar wakilan kasar nan a yanzu.

Ya bayyana cewa da a ce har yanzu yana majalisa, zai tabbata an yi tsayin daga wajen kwato hakkin 'yan Najeriya domin su samu rayuwa ma kyau.

Kara karanta wannan

Akpabio ya saɓa da kwamitin majalisa, ya kare Tinubu kan zargin cushe a dokokin haraji

Hon Gudaji Kazaure da fusata da halin yan majalisa
Hon Gudaji Kazaure tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: House of Representatives/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Hon Gudaji Kazaure ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da DCL Hausa, da aka wallafa a shafin Facebook na kafar.

Ra'ayin Hon Gudaji a kan yan majalisa

A hirar, tsohon dan majalisar Kazaure/Rauni/Gwiwa da Yan Kwashi ya bayyana cewa halin da majalisa ke ciki a yanzu abin takaici ne matuka, musamman yadda ake barin abubuwa suna tafiya ba tare da an kalubalance su ba.

Ya ce:

"Magana ta gaskiya, ina kuka, ina bakin ciki. Ba kuma bakin cikin ba na kan wani matsayi ba. Ina bakin ciki da an wayi gari yau bana majalisa, ina ganin abubuwa suna faruwa a majalisa wanda ba su kamata ba."
"Idan ka duba yanayin majalisa a yau, ba sa fitowa su dage su kwatowa talakawa hakkinsu ta hanyar nunawa gwamnati abubuwan da ta dauko wadanda ba su kamata a."

Ya ce wannan al'amari yana matukar sosa masa rai, wanda da a ce yana majalisa, ba haka al'amura za su gudana ba, domin zai kalubalance su.

Kara karanta wannan

Sanata ya sake taso da batun harin Amurka a Najeriya, ya fadi kuskuren Tinubu

Akwai damuwa a majalisa - Hon Gudaji

Hon Gudaji Kazaure ya ce wasu daga cikin yan majalisa na yin shiru da bakinsu ne sabod ba su da jagorancin da zai mara masu baya wajen tirjewa gwamnati idan an yi ba daidai ba.

Hon Gudaji ya ce yan majalisa sun zama yan amshin shata kawai
Yan majalisa yayin wani zama a Abuja Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Ya bayyana cewa:

"Da ina majalisa, da zan kalubalanci bashi da wannan gwamnati ta ke ciyo wa na tiriliyoyin Nairori. Domin shi ne abu na farko da zan kalubalanta."

Ya bayyana cewa sun yi bincike a baya, kuma sun gano tiriliyoyin kudi da jama'a suka sace daga Najeriya, sannan Shugaban kasa na yanzu, Bola Tinubu ya amince idan ya zo za a karbo kudin domin aiki da su ba tare da an ci bashin ko kwabo ba.

A kan batun dokokin haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kai, ya bayyana cewa da a zamaninsa ne, zai jagoranci a nemi tsige Shugaba Bola Ahmed Tinubu matukar aka tabbatar yana da hannu a zargin cushe da ake yi.

Kara karanta wannan

Ayyukan da gwamnatin Kano za ta saka a gaba bayan Abba ya koma APC

Ya ce:

"Wannan laifin, laifi ne wanda ya kamata a tuhumi gwamnati, a tuhumi Shugaban kasa, a tuhumi su kansu wadanda suka mayar da abin da majalisa ta cire."

Ya ce idan aka yi bincike, Shugaban kasa, aka samu Tinubu da hannu a zargin cushen, to laifin tsigewa ne, kuma da yana majalisa, shi ne zai jagoranci hakan.

"Idan har an same shi da laifi, ni zan yi kuduri na a tsige shugaban kasa, domin doka da oda muke yi a Najeriya."

Hon Gudaji ya gana da Atiku

A baya, kun samu labarin cewa tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya karɓi bakuncin Hon. Gudaji Kazaure, inda suka tattauna kan halin da Najeriya ke ciki da matakan da za a ɗauka a 2027.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɗin kan 'yan siyasa don ceto Najeriya, tare da samar da jagoranci da zai inganta rayuwar al’umma, yayin da jama'a ke kuka da karuwar talauci da rashin tsaro a sassa da dama.

Hon Gudaji Kazaure ya bayyana cewa sun shirya bin tsarin Atiku da shugabannin Arewa don samar da ci gaba da ceto Najeriya daga matsalolin da ta shiga domin a samu farfado da tattalin arziki da inganta tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng