Bayan Zama Sojan Rasha, 'Dan Kano Ya Rasu Yana Gwabza Yaki da Ukraine

Bayan Zama Sojan Rasha, 'Dan Kano Ya Rasu Yana Gwabza Yaki da Ukraine

  • 'Dan jarida Jafar Jafar ya ja hankalin matasan Najeriya kan haɗarin zuwa ƙasar Rasha domin zama soja, bayan mutuwar wani matashi ɗan Kano a fagen yaƙi da Ukraine
  • Ana zargin cewa matashin mai suna Anas Adam ya rasa ransa ne a Rasha, inda aka wallafa sakon jana’izarsa a shafukan sada zumunta a ranar 13, Janairu, 2026
  • Martanin ’yan Najeriya ya nuna ra’ayoyi mabambanta, inda wasu ke ganin ajali ne, yayin da wasu ke alaƙanta lamarin da matsin tattalin arziki da halin da ƙasar ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Dan jarida mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Jafar Jafar, ya yi gargadi ga matasan Najeriya da ke sha’awar barin ƙasar su tafi Rasha domin zama soja da shiga yaƙin da ake yi da Ukraine.

Kara karanta wannan

'Ba talauci ba ne,' Peter Obi ya fadi ainihin matsalar da ke addabar Najeriya

Gargadin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin matasan Afirka, ciki har da ’yan Najeriya, da ke tafiya ƙasashen waje domin shiga yaƙe-yaƙe saboda dalilai na tattalin arziki.

Dan Najeriya da aka ce ya zama soja a Rasha
Anas Adam da ake zargi ya rasu a yakin Rasha da Ukraine. Hoto: Jafar Jafar|Anas Adam
Source: Facebook

Jafar Jafar ya wallafa wannan gargadi ne a shafinsa na Facebook, yana mai cewa ya samu sahihan bayanai kan mutuwar wani matashi ɗan Najeriya da ya tafi Rasha domin shiga aikin soja, inda aka kashe shi a fagen daga.

Dan Kano ya mutu a yakin Rasha

A cikin sakon da aka turawa Jafar Jafar shi kuma ya wallafa, an ce matashin da aka kashe a Ukraine ya bar ’ya’ya da iyali, inda dan jaridar ya yi kira ga matasa da su yi taka-tsantsan.

Legit Hausa ta bibiyi wani shafin Facebook da ake cewa na marigayin mai suna Anas Adam ne, inda sakon da aka wallafa a ranar 13, Janairu, 2026 game da rasuwarsa ya bayyana.

An yi bayani da cewa za a gudanar da addu’ar wannan bawan Allah da misalin ƙarfe 7:00 na safe a kofar gidansu da ke Unguwa Uku, Gidan Fata.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun dimauce bayan fashewar abu mai kama da bam

Martanin ’yan Najeriya kan lamarin

Bayan wallafa sakon rasuwar Anas, ’yan Najeriya da dama sun yi martani kan lamarin ta shafukan sada zumunta, inda ra’ayoyi suka bambanta.

Yazeed Dahiru Mani ya bayyana cewa ba lallai ne irin wannan lamari ya tsoratar da dukkan matasan Najeriya ba, yana mai cewa Allah Ya ji kansa.

Ibrahim Adam Ozil kuwa ya tambaya da cewa:

“Don Allah ta yaya za a bi hanya a je?”

Kalaman Adam Ozil ya nuna yadda wasu ke har yanzu sha’awar tafiyar duk da haɗarinta da gargadin da ake yi game da yin hakan ga matasa.

Wasu sun alaƙanta lamarin da matsalolin shugabanci da tattalin arziki, inda Abba Haruna Muhammad ya ce zaluncin shugabanni da wahalar rayuwa na sa tunanin matasa ya sauya daga alheri zuwa akasin haka.

Dan Najeriya da wani sojan Rasha a kasar
Anas Adam da wani sojan Rasha a fagen daga. Hoto: Jafar Jafar
Source: Facebook

Aminu Usman ya kuma nuna takaicinsa, yana mai cewa Allah Ya isa tsakaninsu da shugabanni da yake zargin su da haddasa talauci da wahala.

Kara karanta wannan

Bayan jirgi marar matuki ya hallaka sojoji, rundunar ta fadi matakin da ta dauka

Sani Garba Ismuhu ya yi addu’ar rahama ga marigayin, yana mai bayyana shi a matsayin mutumin kirki da ya san shi kafin ya tafi kasar Rasha.

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun Najeriya sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.

Dakarun Najeriya sun bayyana cewa sun samu labarin cewa 'yan bindiga sama da 100 sun taru a daji suna shirya yadda za su kai hari.

A yayin artabun da aka yi, sojojin Najeriya sun sanar da kashe 'yan ta'adda da dama ciki har da dan bindiga da ake kira Gwaska Dan Karami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng