An Hango Sauki: Ana So Tinubu Ya Sa Tallafin Danyen Mai, a Rage Kudin Fetur
- 'Yan kasuwar fetur sun ce hanya ɗaya tilo da za a kare ’yan Najeriya daga tashin farashin lita ita ce saka tallafin gwamnati a bangaren danyen mai
- Kungiyar IPMAN ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya amince a saka tallafi a danyen mai tare da faɗaɗa tsarin cikin da Naira da matatun Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa bayan matatar Dangote ta ƙara farashin fetur, an fara hasashen cewa litar mai na iya kaiwa N1,000 a wasu sassan ƙasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Dillalan man fetur a Najeriya sun nuna damuwa kan tashin farashin fetur da ake fuskanta, suna cewa wajibi ne gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki domin rage wa ’yan ƙasa raɗaɗin ƙarin farashi.
Sun bayyana cewa sa tallafi a farashin danyen mai da ake sayar wa matatar Dangote da sauran matatun mai na cikin gida zai taimaka wajen daidaita farashin fetur a kasuwanni, musamman a lokutan da farashin danyen mai ke tashi a duniya.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa wannan kira na zuwa ne bayan matatar Dangote ta ƙara farashin fetur, lamarin da ya haifar da ƙarin farashin a yawancin gidajen mai a faɗin ƙasar.
Kiran kungiyar IPMAN kan tallafin mai
Kungiyar Independent IPMAN ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya duba sa tallafi a danyen mai da ake sayar wa matatun cikin gida.
Kakakin IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce idan aka sa tallafi a danyen mai, hakan zai taimaka wajen rage tasirin tashin farashin fetur da ka iya biyo bayan hauhawar farashin danyen mai a duniya.

Source: Getty Images
Ya bayyana cewa IPMAN na kuma son a faɗaɗa tsarin cikin danyen mai da Naira, ba ga matatar Dangote kaɗai ba, har da sauran matatun da ke aiki a ƙasar.
Dalilan buƙatar tallafin danyen mai
Ukadike ya ce farashin danyen mai yana sauyawa akai-akai a kasuwannin duniya, kuma duk wani canji kai tsaye yana shafar farashin fetur, dizal da sauran kayayyakin mai.
Ya ce idan gwamnati ta samar da wata yarjejeniya ta musamman kan farashin danyen mai ga matatun cikin gida, hakan zai zama kariya daga tashin farashi, tare da tabbatar da daidaito ko da farashin danyen mai ya tashi a duniya.
A cewarsa, tallafin danyen mai zai hana hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka a cikin gida, domin fetur na taka muhimmiyar rawa wajen jigilar kaya da ayyukan yau da kullum.
Kudin man fetur ya tashi a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa matatar Dangote da ke Legas ta sanar da ƙarin farashin fetur daga N699 zuwa N799 kan kowace lita.
Wannan ƙarin farashi ya sa lita ta tashi a yawancin gidajen mai, inda a wasu sassan Lagos kudin ya kai tsakanin N830 zuwa N859 kan kowace lita.
Kamfanin NNPC Limited ya sayar da fetur a N849 kan kowace lita a hanyar Lagos–Ibadan, yayin da gidajen mai na MRS suke sayarwa a N839.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

