An Sanya Lokacin Jana'izar Sheikh Usman Rigi Rigi, 'Masoyin Annabi Ya Rasu'

An Sanya Lokacin Jana'izar Sheikh Usman Rigi Rigi, 'Masoyin Annabi Ya Rasu'

  • Fitaccen malamin Musulunci dake Zaria, Sheikh Khalifa Usman Kusfa wanda aka sani da Rigi-rigi, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya
  • An ce za a gudanar da sallar jana'izar marigayin a Kusfa da ke Zaria a yau Litinin, inda ake sa ran dubun-dubatar musulmi za su halarci salla da birne shi
  • Mutuwar Sheikh Rigi-rigi ta girgiza al'ummar Musulmi a Najeriya, musamman ganin yadda ya shahara da nashi salon wa'azin mai cike da barkwanci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - A ranar 2 ga Fabrairun 2026 ne aka samu labarin rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Khalifa Usman Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-rigi.

Mutuwar Sheikh Usman Rigi Rigi ta girgiza al'ummar Musulmi, musamman wadanda ke a Arewacin Najeriya la'akari da kaurin sunan da malamin ya yi.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Rigi Rigi ya rasu

Malamin Musulunci, Sheikh Usman Kusfa Rigi Rigi ya rasu
Marigayi Sheikh Khalifa Usman Kusfa (Rigi Rigi) a wajen taron Mauludi. Hoto: Sheikh Usman Rigi Rigi
Source: Facebook

Sheikh Usman Kusfa Rigi Rigi ya rasu

Tun da fari, jaridar Aminiya ce ta ruwaito cewa fitaccen malamin, dan asalin garin Zaria, jihar Kaduna, ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

An kuma samu rahoto cewa Sheikh Rigi Rigi ya rasu a gadon asibiti a daren Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, kuma an shirya jana'izarsa a ranar Litinin.

Malam Abubakar Danyaro, wanda ya kasance surukin Sheikh Rigi Rigi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce za a yi jana'izar bayan sallar La'asar, a kofar gidan malamin da ke Kusfa, Zaria.

Surukin ya ce Sheikh Khalifa Usman ya kwashe tsawon lokaci yana jinya a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna, kafin daga bisani a mayar da shi wani asibitin kudi da ke Unguwar Barnawa, inda a nan Allah ya karbi rayuwarsa.

Tuna baya: Dalilin sanya masa sunan 'Rigi Rigi'

Kara karanta wannan

Yadda aka gyara Tudun Biri bayan sojojin Najeriya sun yi kuskuren jefa bam a taron Maulidi

A wata hira da jaridar DCL Hausa ta wallafa a shafinta na YouTube, Sheikh Khalifa Usman Kusfa ya bayyana dalilin da ya sa aka sanya masa sunan 'Rigi Rigi.'

Sheikh Rigi Rigi ya ce:

"Game da suna Rigi Rigi, wani lakabi ne da mutane suka sanya mani shi. Rigi Rigi kamar hadari ne, da ya saukar da ruwa mai yawa, irin ruwan dare mai gama duniya, saboda suna samun ilimai masu dimbin yawa daga wajena, shi ne ake ce mun rigi rigi.
"Ina jin dadi idan aka kira ni da Attalili Attagazuti, saboda sunan waliyyi, ko a kira ni da Rigi Rigi, ko a ce mun Rugum, ko a ce mun Na'Annabi, to wannan na fi jin dadi."

An yi jimamin rasuwar Sheikh Rigi Rigi

Legit Hausa ta tattaro abubuwan da mutane suka fada game da rasuwar wannan fitaccen malamin Musulunci:

Ashiru Sale Dan Daura ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"Wallahi, duniya ta yi babban rashi, duk wani masoyi zaiyi alhini, cikin alhini muke sanar daku Allah ya yi wa Sheikh Usman Kusfa Rigirigi na Annabi Muhammad (S.A.W.) rasuwa cikin wannan dare.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi rashi: Farfesa kuma malamin addini ya yi bankwana da duniya

"Jana’iza ƙarfe huɗu da rabi (4:30 PM) a filin Locos, wajen da yake yin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W., yau Litinin, Allah ya yi masa Rahama, alfarmar Annabi Muhammad S.A.W. Amin."

Jan Kondo:

"Allah ya jikansa amen. Kowa ya san cewa wannan bawan Allah bai da matsala da kowa.
"Wa'azinsa yake ba tare da kiran wani ko wata ba. Allah yayi masa rahama."

Sani Idrisa:

"Allah ya jikan shi da rahama. Ya kyauta namu bayan nasu."

Bllal Bsse:

"Hasbunallahu wani'mal wakil. Allah yasa mu cika da imani."

Yaya Mamman:

"Allah sarki rayuwa ba tabbas, Masoyin Annabi ya rasu, Allah ya yafe masa."

Salihu B Lamido:

"Allah masa rahama ya yafe masa kura kurensa. Allah sarki rayuwa kenan."

Alkali Zaria ya ziyarci Sheikh Rigi Rigi

A wani labari, mun rahoto cewa, babban malamin Izala, Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya ziyarci malamin Darika, Sheikh Usman Rigi Rigi a Zariya.

'Yan Izala da dama sun fito sun nuna cewa bai kamata Sheikh Abubakar Salihu ya kai ziyara ga malamin Darikar ba saboda irin salon wa'azin da yake yi.

Sai dai Sheikh Abubakar Salihu ya ce sun dauki lokaci yana tattaunawa da Rigi Rigi musamman kan abubuwan da yake fada da ake ganin sun saɓa hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com