Musulunci Ya Yi Rashi: Farfesa kuma Malamin Addini Ya Yi Bankwana da Duniya

Musulunci Ya Yi Rashi: Farfesa kuma Malamin Addini Ya Yi Bankwana da Duniya

  • An tabbatar da rasuwar fitaccen malamin Musulunci a Ilorin da ke Jihar Kwara, a ranar Juma’a 30 ga Janairu, 2026
  • Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya nuna alhini tare da aikawa da sakon ta’aziyya ga Sarkin Ilorin, shugabannin Musulmi da iyalan marigayin
  • Gwamnatin Kwara ta ce marigayin ya bar gagarumar tarihi a ilimi da zaman lafiya, tare da roƙon Allah ya sanya shi a Aljannar Firdaus

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Duniyar Musulunci ta yi babban rashi da aka sanar da rasuwar malamin addini kuma Farfesa a jihar Kwara.

An tabbatar da rasuwar Farfesa Yusuf Lanre Badmus a ranar Juma'a 30 ga watan Janairun 2026 da muke ciki.

Malamin Musulunci a Kwara ya bar duniya
Marigayi Farfesa Lanre Badmus da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak na jihar Kwara. Hoto: MSSN Kwara Area Unit.
Source: Facebook

Malamin Musulunci ya rasu a Kwara

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye ya sanyawa hannu wanda gwamnatin jihar ta wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Limamai da fastoci za su dara a Bauchi, Gwamna Bala ya sanya su a sabon tsari

Sanarwar ta ce gwamnatin Kwara ta nuna jimami kan rasuwar malamin wanda ya ba da gudunmawa ga al'umma da kuma addinin Musulunci.

Gwamnan Abdulrahman Abdulrazak ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, Sarkin Ilorin, shugabannin Musulmi da jihar Kwara baki daya.

Addu'o'i da gwamnan Kwara ya yi

Ya roki Ubangiji ya gafarta masa kuma ya saka masa da gidan aljanna firdausi da kuma kare iyalansa baki daya.

A cikin sanarwar, gwamnatin Kwara ta ce:

"Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Farfesa Yusuf Lanre Badmus, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran al’umma.
Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga Mai Martaba Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari, da shugabannin Musulmi a Jihar Kwara, iyalan Markaz, da kuma iyalan marigayin Farfesa Badmus.
Gwamna AbdulRazaq ya ce marigayin ya bar kyakkyawan tarihi a matsayinsa na shahararren malami kuma mai fafutukar zaman lafiya, wanda ya shafe shekaru yana bayar da gagarumar gudunmawa ga Jihar Kwara da Ilorin musamman.
Ya roƙi Allah da ya yi wa Farfesa Yusuf Lanre Badmus rahama, ya sanya shi a Aljannar Firdaus, tare da kiyaye iyalansa a kan alheri."

Kara karanta wannan

Majalisa ta ware jiha 1 a Arewa da take so jami'an tsaro su kai jerin hare hare

Gwamnan Kwara ya yi jimamin malamin Musulunci a Kwara
Gwamna Abdulrahman Abdulrazak na jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government.
Source: Twitter

Sarkin Musulmi ya tura sakon jaje

Har ila yau, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi jimamin rashin malamin inda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalansa da al'ummar Musulmi, cewar NTA News.

Sarkin Musulmi ya bayyana bakin ciki bisa rashin gogaggen malamin inda ya ce tabbas an yi rashin da maye gurbinsa zai yi matukar wahala.

Ya ce babu yadda aka iya da ikon Allah amma mutuwar malamin ta kawo gibi ga Musulunci a Najeriya da duniya baki daya.

An kama malamin Musulunci a Kano

Mun ba ku labarin cewa 'yan sandan Kano sun gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a gaban kotu bisa zargin karkatar da filayen gwamnati da na al’umma.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ce-ce-ku-ce a zaman kotun bayan lauyansa ya ce akwai wata shari’a makamanciyarta a kasa.

Bayan caccaka tsinke da aka yi a zaman da ya gudana, kotu ta bayar da belin malamin tare da ɗage shari’ar zuwa wani lokaci na daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.