Sanusi II Ya Koma Kano a 'Matsayin Sarki', Aminu Ado Bayero Ya Yi Zaman Fada
- Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya dawo Kano bayan gwamnatin jihar ta jaddada matsayinsa a matsayin halastaccen sarkin jihar
- A yayin da Sanusi II ke dawowa daga tafiya, Aminu Ado Bayero shi ma ya gudanar da zaman fada tare da karɓar gaisuwar jama’a a Kano
- Halin da ake ciki ya nuna ci gaba da ikirarin sarautar Kano daga bangarorin biyu, inda kowanne ke zaune a fada ta daban yana jagorantar jama'a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mai martaba Khalifa Dr Muhammadu Sanusi II ya dawo jihar Kano a ranar Juma’a, 30, Janairu, 2026, bayan wata tafiya da ya yi zuwa Kudancin kasar nan.
Dawowar tasa ta zo ne jim kadan bayan gwamnatin Jihar Kano ta fito karara ta bayyana cewa shi ne halastaccen Sarkin Kano, ba Aminu Ado Bayero ba, a ci gaba da rikicin da ya dabaibaye sarautar Kano.

Source: Twitter
A lokaci guda kuma, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ci gaba da gudanar da harkokin fada, inda ya wallafa a X cewa ya karɓi gaisuwar Juma’a a gidan Nasarawa.
Tafiyar da Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi
A yayin tafiyar da ya yi kafin dawowarsa Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Otunba Adekunle Ojora a jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayi Otunba Ojora shi ne Olori Omo Oba na Legas, kuma ya rasu da safiyar ranar Laraba yana da shekaru 93.
A yayin ziyarar, Sanusi II ya gana da iyalan Otunba Ojora, wanda surukin Sanata Bukola Saraki ne, tare da sauran ’yan uwa da makusanta.
Haka kuma, fadar Sanusi II ta wallafa a Facebook cewa ya haɗu da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, da wasu manyan baki.

Source: Facebook
Mai martaba Sanusi II ya dawo jihar Kano

Kara karanta wannan
Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano
Bayan kammala ziyarar ta’aziyya, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya dawo Kano, inda magoya bayansa da dama suka nuna farin ciki da dawowarsa.
Dawowar ta sake jan hankalin jama’a game da makomar rikicin sarautar Kano, musamman ganin yadda gwamnati ta sake jaddada matsayinsa a wajenta.
Aminu Ado Bayero ya yi zaman fada
A bangare guda kuma, mai martaba Aminu Ado Bayero ya gudanar da zaman fada a ranar Juma’a, 30 ga Janairun 2026, inda ya fito domin karɓar gaisuwar Juma’a daga hakimai, dagatai, masu unguwanni da jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa daga bisani mai martaba Aminu Ado Bayero ya karɓi baki na musamman a fadarsa ta gidan Nasarawa da ke birnin Kano.
Wannan mataki ya nuna cewa bangaren Aminu Ado Bayero na ci gaba da ikirarin sarautar Kano, duk da matsayar da gwamnatin jihar ta dauka.
Abba zai warware rikicin Kano
A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana daukar matakai domin warware rikicin sarautar Kano.
Kwamishinan yada labaran Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai a jihar.
Hon. Waiya ya bayyana cewa mutanen Kano za su fara shan romon dimokuradiyya yadda ya kamata bayan Abba Kabir ya shiga APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
