Iyalan Sojojin da Suka Shirya Juyin Mulki Sun Yi wa Tinubu Maganar Afuwa
- Iyalan wasu manyan jami’an soji da ake tsare da su bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun fara neman afuwa
- An ce jami’an da suka kai akalla 16 suna jiran hukuncin kotun soja bayan kammala dogon bincike da rundunar tsaron Najeriya ta yi game da su
- Iyalan sojojin sun roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya nuna tausayi, la’akari da halin da iyalansu ke ciki da kuma matsayinsa a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Iyalan wasu jami’an sojin Najeriya da ake tsare da su bisa zargin shirya yunkurin juyin mulki sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran hukumomi da su sassauta hukunci a kan ‘yan uwansu.
Rahotanni sun nuna cewa iyalan na kai-komo ofisoshin manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa domin neman a shiga tsakani.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa hakan na zuwa ne bayan kammala binciken da aka ce ya tabbatar da zargin, inda aka mika rahoto ga shugaban kasa.
Zargin da ake yi wa jami’an sojin
Premium Times ta ce akalla jami’an soji 16, daga mukaman Kyaftin har zuwa Birgediya Janar, ne ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu.
An ce an kama jami’an tun watan Oktoba, 2025, inda aka tsare su a hannun Hukumar Leken Asirin Tsaro ta Soji yayin da ake shirin gurfanar da su a yanzu.
Iyalan sojoji sun yi kira ga Tinubu
A wata hira ta musamman, wani dan uwa ga daya daga cikin manyan jami’an sojin ya ce iyalan ba su da wani zabi illa neman afuwa.
Ya ce laifin yana da girma a karkashin dokokin soji da na kasa, amma jami’an ‘yan uwansu ne kuma suna da iyalai da suke kula da su.
Ya roki Shugaba Tinubu, a matsayinsa na Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya, da ya tausaya musu ya sassauta musu.
Wani dan uwa daban, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun shiga rudani matuka bayan jin labarin tsare ‘ya’yansu da zargin juyin mulki.

Source: Twitter
Ya ce yanzu burinsu shi ne rokon al’ummar Najeriya da shugaban kasa da su musu afuwa kar a kashe su, musamman ganin cewa wasu daga cikin jami’an suna da ‘ya’ya kanana.
Wani kwararre kan harkokin tsaro, Abdullahi Garba, ya bukaci a gudanar da shari’a a fili kuma cikin adalci ba tare da wani boye-boye ba.
Ra’ayin wani tsohon jami’in soja
Tsohon jami’in soja, Manjo Bashir Galma mai ritaya, ya bayyana cewa yunkurin juyin mulki abu ne mai hadari sosai a Najeriya.
Ya ce duk wata sana’a tana da nata hadari, inda ya jaddada cewa su da suka shiga juyin mulkin 1983 sun yi sa’a ne kawai abin ya yi nasara.
Yadda aka shirya kashe Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa an samu wasu bayanai game da yunkurin juyin mulki da aka yi a Najeriya a shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Birgediya Janar Sadiq: Bayanan da muka sani kan sojan da ake zargi da hannu a 'juyin mulki'
Rahotanni da suka fito sun nuna cewa ana zargin sojojin da suka shirya juyin mulkin sun tsara yadda za a kashe wasu manyan mutane.
A bayanin da Legit Hausa ta samu, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima na cikin wadanda aka shirya kashewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

