An Fara Sabon Yaki: Sojoji Sun Kutsa Daji, Sun Yi wa 'Yan Bindiga Jina Jina
- Rahoto ya nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da Operation Igbo Danu domin fatattakar ‘yan ta’adda a dazukan Kwara
- Hadin gwiwar dakarun Najeriya da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro sun kai ga rushe sansanonin ‘yan ta’adda
- Shugabannin sojin sun bukaci jama’a su ci gaba da ba da sahihan bayanai domin kakkabe masu daukar nauyin ta’addanci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da wani sabon farmaki mai suna Operation Igbo Danu domin murkushe ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan jihar Kwara.
Rundunar ta kai farmaki a tsakanin 23, Janairu, 2026 zuwa 29, Janairu, 2026, inda sojojin suka samu gagarumar nasara wajen tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda a dazuka da yankunan karkara.

Source: Facebook
Sojoji sun wallafa a X cewa farmakin ya zo ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke kara zage damtse wajen dakile ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa ta Tsakiya.
Sojojin da suka tsara farmakin
Ayyukan Operation Igbo Danu sun gudana ne karkashin jagorancin Manjo Janar Chinedu Nnebife, Babban Kwamandan runduna ta 2 ta sojin Najeriya kuma Kwamanda a Operation Fansan Yamma.
Haka kuma, Birgediya Janar Nicholas Rume, Kwamandan runduna ta 22, ya taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da aiwatar da farmakin.
Sojojin sun samu cikakken goyon baya daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, lamarin da ya kara karfin hadin gwiwa da saurin daukar mataki.
Sojoji sun farmaki 'yan bindiga
A yayin farmakin, sojojin sun kai hare-hare kan wasu maboyar ‘yan ta’adda da dama, inda suka kashe wasu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.
Jaridar Punch ta wallafa cewa sun lalata sansanonin 'yan bindiga gaba daya, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan barin yankunan da suke fakewa.
A Ifelodun, sojoji sun kwace Garin Dandi, wani sanannen sansanin ‘yan ta’adda, inda aka rusa hanyoyin jigila da ajiyar kayan aiki da suke dogaro da su.

Source: Facebook
Sojoji sun ceto mutane a Kwara
Sojojin sun kuma kai farmaki wasu sansanonin da a baya ba a iya kaiwa saboda wahalar hanya, inda aka lalata wuraren boye kayayyakin ‘yan ta’adda.
Duk da matsalar hanya da dazuka masu duhu, sojojin sun ci gaba da matsin lamba, tare da hana ‘yan ta’adda motsi da walwala.
A wasu wurare, sojojin sun cafke wadanda ke kokarin tserewa, tare da ceto mutane da dama da aka sace daga sansanonin ‘yan ta’adda a jihar.
An kama wanda ya mallaki bindiga
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da ya mallaki bindiga ba tare da izinin hukuma ba.
Kakakin 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da cewa an kama matashin ne bayan ya lakadawa mahaifiyarsa duka.
Mahaifiyar ta ce tun bayan dawowa daga hutun karshen shekara da ya yi ya fara nuna wasu alamu marasa kyau, inda ta samu bindiga a jakarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

