Mazauna Kano Sun Dimauce bayan Fashewar Abu Mai Kama da Bam
- Mazauna Rijiyar Lemo a Kano sun shiga ruɗani bayan fashewar wani abu da ake zargin bam ne, har ya jikkata bayin Allah
- Mazauna yankin sun bayyana cewa mutane uku sun jikkata, yayin da wani ya rasa hannu sakamakon fashewar abin
- Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma'a, 30 ga watan Janairu da kusan 5:20 na yamma, jami'an tsaro sun kai dauki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mazauna Rijiyar Lemo da ke birnin Kano sun shiga ruɗani bayan fashewar wani abu da ake tsammanin bam ne, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Juma’a a yankin a layin gidan man Azman, wannan lamari ya tayar da hankalin jama’a a yankin.

Source: Original
Wani mai suna Buhari Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa jama’a sun yi zargin ko bam ne ya tashi, kasancewar karar fashewar ta yi ƙarfi matuƙa.
Abu ya fashe a jihar Kano
Ɗaya daga cikin mazauna yankin Rijiyar Lemo, layin Azman, gadar Sa’idu, ƙarshen kwalta, ya shaida wa majiyar Legit cewa suna zaune lafiya, kawai sai suka ji ƙarar wani abu mai ƙarfi.
Ya ce karar ta sa mutane suka firgita tare da neman mafaka, domin ba su san ainihin abin da ya faru ba, yayin da shi da wasu suka durfafi wajen domin kai dauki.
Mutumin mai suna Mustapha Muhammad Batoyi ya bayyana cewa:
“Muna zaune a gefe, sai muka ji ƙarar wani abu mai ƙarfi, abu ya fashe. Nan take muka zo da gudu domin mu kawo ɗauki. Mutum uku ne a ciki, kowannensu ya jikkata.'
"Amma shi ainihin mai rumfar da abin ya same shi, abin ya taba shi sosai, domin har an yanke masa hannu. Haka kuma kafafuwansa sun samu matsala.”
Jami’an tsaro sun kai ɗauki a Kano
Batoyi ya ƙara da cewa abin fashewar ya tashi ne a wajen ‘yan gwangwan, kuma tuni jami’an tsaro suka kewaye wajen domin zurfafa bincike bayan sun kawo agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.

Source: Twitter
A kalamansa ya ce:
“Ƙarar da muka ji ba mu sani ba ko gas ne ko bam ne, Allah ne kawai Ya san abin da ya fashe a wajen.”
Ya ci gaba da cewa:
“’Yan sanda sun zo, mataimakin kwamishina ya zo, shi ma AIG na Kano ya zo wurin, manyan ‘yan sanda da dama sun hallara. Sun daura kyalle domin hana shiga wurin. Har sun tare dukkan hanyoyi guda uku, ba shiga ba fita.”
Ya bayyana cewa duk da jami’an ‘yan sandan sun tafi daga bisani, sun ɗauki bidiyo da sauran abubuwan da suka ga ya dace domin taimakawa bincike.
Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan fashewar abin da ya jikkata mutane uku ba.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2
An kama abin hada bam a Kano
A baya, mun wallafa cewa kakakin rundunar ‘yan sanda ta Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kama buhunan da ake zargin sun kunshi kayan fashe wa.
Ya ce a ranar Litinin, jami’an da ke caji ofis na Rijiyar Lemo bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda sun gudanar da bincike a gidan da ke Tudun Bojuwa, a karamar hukumar Fagge.
CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kara da cewa kwararrun jami’an rundunar masu kula da kayan fashe wa sun tantance tare da gano abubuwan fashewa a buhunan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

