Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba Ya Bayyana Wanda zai Ci Gaba da Zama Sarkin Kano
- Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC ta sake taso da jita-jita kan kujerar Sarkin Kano da ake ta takaddama a kai
- Wasu na hasashen cewa sauya shekar gwamnan na iya jawowa ya sauke Muhammadu Sanusi II daga kan kujerar sarauta
- Sai dai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito karara ya raba gardama kan jita-jitar da ake ta yadawa tun bayan komawarsa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Biyo bayan sabon hadewar siyasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi da gwamnatin tarayya, an sake fara rade-radi kan rikicin masarautar Kano da ya dade yana gudana.
Ana ta hasashe da maganganu cewa ko sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC za ta iya sauya makomar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattauna da mai magana da yawun bakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, kan jita-jitar da ake yadawa a ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026.
Me Gwamna Abba ya ce kan sauya Sarkin Kano?
Gwamna Abba ya yi watsi da duk wata magana da ke cewa sauyin siyasar na iya kaiwa ga sauke Sarkin Kano, inda ya jaddada cewa matsayin Sarkin nan nan daram ne kuma bai sauya ba.
Ya bayyana cewa “Ko kadan wani shiri ko yarjejeniya” da za ta kai ga cire Muhammadu Sanusi II daga karagar mulki.
"Babu wani shiri na maye gurbin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. An nada sarkin ne bayan soke dokar masarautu, kuma babu wani shiri a matakin zartarwa na sake yin gyara ko sauyi.”
"An nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi bisa doka bayan soke dokar, kuma wannan sauya sheka zuwa APC ba zai sauya komai ba. Sarkin Kano shi ne Sarkin Kano. Babu wani shiri, babu wata niyya ta maye gurbinsa.”
- Sanusi Bature Dawakin Tofa
Gwamna ya bukaci a yi watsi da jita-jita
Gwamna Abba ya bayyana rade-radin da ke yawo a matsayin jita-jita marasa tushe da wasu mutane ke yadawa “wadanda ba su yi wa jihar Kano fatan alheri”.
"Ya kamata mutane su yi watsi da irin wadannan jita-jita. Dole ne a bambanta tsakanin hukumomi. Masarauta ba ta siyasa ba ce. Abin da Mai Girma Gwamna ya yi shi ne mayar da martaba da kimar da masarautar ta rasa.”
- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Source: Facebook
Shin Gwamna Abba na tattaunawa da Aminu Ado?
Game da ko gwamnatin na tattaunawa da bangaren Aminu Ado Bayero ko wadanda ke adawa da dawo da Sanusi II, Sanusi Bature ya ce ba a fara irin wannan tattaunawa ba.
Ya ce: “Ba a fara ba tukuna,” amma ya kara da cewa gwamnatin na rokon Aminu Ado Bayero da magoya bayansa da su fifita zaman lafiya.
“Muna rokonsa da masu mara masa baya da su taimaka saboda zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban tattalin arzikin jihar Kano, su nesanta kansu daga ikirarin jiran a mayar da su kan karagar mulki."
- Sanusi Bature Dawakin Tofa
Gwamna Abba ya yi sababbin nade-nade
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sababbin nade-nade bayan komawarsa jam'iyyar APC.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da sababbin nade-nade da karin girma ga wasu manyan jami’ai a jihar Kano.
Nade-naden na cikin kokarin gwamnatin jihar na sake fasalin hukumomi domin su yi aiki yadda ya dace wajen bauta wa al’ummar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

